Rayuka 15 sun salwanta yayin wani artabu a gidan yari
Hukumomin tsaro sun tabbatar da cewa, wani bakin artabu da ya auku tsakanin fursunoni a ranar Lahadin da ta gabata ya salwantar da rayukan mutane 15 dake daure a gidan kaso na jihar Amazonas dake Arewacin kasar Brazil.
Kamar yadda wani jami'in hukumar gidajen yari na kasar Brazil Kanal Marcos Vinicius Almeida ya shaidawa manema labarai, bakin gumurzu ya barke da misalin karfe 11.00 na safiya a daidai lokacin ziyarar fursunoni a gidan dan Kanden dake yankin babban birnin Manaus.
A yayin da hukumomi masu ruwa da tsaki suka nutsa cikin bincike domin gano musabbabin wannan mummunar kasassaba, Kanal Almeida da yawa daga cikin fursunonin sun riga mu gidan gaskiya ta hanyar suka da caccaka da makamai masu kaifin gaske.
Kanal Ameida ya ce zaburar jami'an tsaro da kuma tashi na zumbur cikin kankanin lokaci domin tunkarar wannan mummunan lamari ya taimaka kwarai da aniyya wajen kawo rangwami na asarar da ta'addanci ya haddasa.
An tunatar da mai karatu cewa makamancin wannan ta'ada ta barkewar bakin gumurzu har ta tsawon kimanin awanni ashirin ta salwantar da rayukan fursunoni 56 yayin aukuwar ta a gidan kason na na jihar Amazonas a shekara ta 2017.
KARANTA KUMA: Ba zan yi gaggawar nadin mukamai ba - Gwamnan Nasarawa
Kididdigar alkaluma ta tabbatar da cewa, kasar Brazil ta kasance akan sahu na uku cikin jerin kasashe masu tarin fursunoni yayin da adadin fursunonin ta a shekarar 2016 suka kai kimanin 726,712.
Kasar Brazil ta yi fice a fagen aukuwar miyagun laifuka kamar safara da kuma fataucin miyagun kwayoyi, fashi da makami da sauran miyagun laifuka masu haddasa cika da batsewar gidajen yari.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng