Daga zuwa biyan kudin fansa, yan bindiga sun yi garkuwa da hadimin gwamnan Katsina
Guda daga cikin tsofaffin hadiman gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari, Kwamared Bashir Usman Ruwan Godiya ya fada hannun masu garkuwa da mutane da sanyin safiyar Juma’a, 31 ga watan Mayu na shekarar 2019.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ruwan Godiya, wanda Malami ne a kwalejin kimiyya da fasaha ta jahar Katsina, ya fada hannun yan bindigan ne a yayin da yaje wajensu domin biyan kudin fansan wani abokin aikinsu da yan bindigan suka yi garkuwa dashi a ranar Alhamis.
KU KARANTA: Yayan majalisar dokokin jahar Imo sun zabi sabon kaakakin majalisa
Rahotanni suna bayyana cewa jim kadan bayan yan bindigan sun kama Ruwan godiya, sai suka tuntubi iyalansa inda suka nemi a biyasu karin kudin fansa kafin su sakoshi tare da abokin aikin nasa.
Idan za’a tuna wasu gungun yan bindiga sun yi garkuwa da malamin kwalejin kimiyya da fasaha ta Hassan Usman dake jahar Katsina, Dakta Bello Birchi, a gidansa dake kan titin zuwa garin Dutsanma a kauyen Tashar Bara’u cikin karamar hukumar Birchi, a daren Alhamis.
Shugaban kungiyar Malaman kwalejin kimiyya da fasaha, Dakta Sabi’u Yau Abdullahi ne ya tabbatar da sace abokin aikin nasu, inda yace lamarin ya jefa kafatanin malaman kwalejin cikin halin dimuwa, alhini da jimami.
Kimanin watanni biyu kenan yan bindiga sun tsananta kai hare hare a jahar Katsina, musamman a kananan hukumomin Kankara, Dutsanma da kuma Batsari, da kauyukan dake zagaye dasu.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng