Yadda sojoji suka yi dirar mikiya domin kwace giyar da Hisba ta kama a Jigawa

Yadda sojoji suka yi dirar mikiya domin kwace giyar da Hisba ta kama a Jigawa

A ranar Laraba, wasu jami'an sojojin Najeriya sunyi dirar mikiya a hedkwatan Hukumar Hisbah da ke Dutse a Jihar Jigawa domin karbo giya da jami'an hisbah suka kwato a cewar wani jami'in na hisbah.

Kwamandan Hisbah na jihar, Ibrahim Dahiru ya shaidawa manema labarai cewa jami'ansa sun kwato giyan ne a daren ranar Laraba a wani dandali da ake kira Nasara a unguwar Takur Adu'a.

Yayin sumamen an kwace katon din giya 70 da kwallaben giya 13,920 inda daga bisani aka kai su ofishin Hisbah da ke garin Dutse.

Sai dai Mr Haruna ya ce bisani sojojin da ke atisayen 'Operation Salama' sun zo ofishin na Hisbah domin kwace giyan.

Yadda sojoji suka kai farmaki ofishin Hisbah don kwato giya a Jigawa

Yadda sojoji suka kai farmaki ofishin Hisbah don kwato giya a Jigawa
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Masana sun bayyana kudin sabuwar motar shugaba Buhari

"Bana nan lokacin da suka zo amma wani ma'aikacin mu ya kira ni ya fada min sojoji dauke da makamai sun zo tare da mai giyar sunyi kutse a ofishin mu. Sai dai sojojin ba su tafi da giyar ba saboda na rufe su a ofishi na.

"Na kira kwamishinan 'yan sanda da direktan SSS na fada masu abinda ke faruwa inda su kayi gaggawar daukan matakin tsawata wa sojojin.

"Ba mu tafi barikin soji kwato giya ba kuma ba mu tare motar giya ba. Mun je aiki ne kamar yadda muka saba inda muka kwato giyar. Ban ga dalilin da zai sa sojojin su dauki matakin da suka dauka ba," inji Dahiru.

Ya kara da cewa za a gurfanar da mai giyan a gaban kuliya.

Kakakin 'yan sandan jihar Jigawa, Bala Senchi ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Amma ya ce sojojin ba su kai farmaki ofishin Hisbah ba. "Sun tafi sintiri ne kamar yadda suka saba kuma ba su ci zarafin kowa ba kuma ba su dauki komi a ofishin Hisban ba kamar yadda kwamandan Hisban ya tabbatar min."

Sai dai wani soja mai suna M.I. Ikemba ya shaidawa Daily Trust cewa zargin da ake musu ba gaskiya bane.

Ya ce ya dauki mataki ne bisa rahoton da ya samu na cewa 'yan Hisbah sunyi kutse gidansa sun kwace giya.

"A lokacin da suka isa gida na sun bale kofar inda suka samu matar aure tsirara. Na tafi ofishin Hisbah ne domin inyi magana da kwamanda amma ban same shi ba. Daga baya na aika direba na tare da mai giyan da aka kwace domin suyi magana. Ba farmaki na kai ofishin su ba kamar yadda Hisbah su kayi ikirari," inji Sojan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel