Diyar Atiku ta ce ba za ta taba mantawa da mulkin APC ba

Diyar Atiku ta ce ba za ta taba mantawa da mulkin APC ba

Dakta Fatima Atiku, Diyar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar ta ce ba za ta taba mantawa da aikin da tayi a matsayin Kwamishinan lafiya a karkashin gwamna Muhammadu Bindow da ya kammala mulki ba.

Fatima tana daya daga cikin masana makaman aiki da Bindow ya nada mukami domin taimaka masa kawo sauyi a fanin lafiya na jihar Adamawa.

Ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a ranar Alhamis a Yola cewa an samu nasarori da yawa a fanin lafiya a zamaninta da suka hada da shirin inshora ta lafiya, Tsarin samar lafiya na jihar Adamawa, Rajistan masu dauke da Kansa da sauran su.

Diyar Atiku ta ce ba za ta taba mantawa da mulkin APC ba

Diyar Atiku ta ce ba za ta taba mantawa da mulkin APC ba
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Masana sun bayyana kudin sabuwar motar shugaba Buhari

"Ba zan taba mantawa da shekaru hudu da nayi ina aiki a nan ba; wannan shine karo na farko da nayi aikin gwamnati kuma na koyi abubuwa masu dimbin yawa saboda cudanya da jama'a da na ke yi.

"Nayi farin ciki sosai saboda an bani dama kuma al'ummar Adamawa sun amfana da ayyukan da muka yi," inji tsohuwar kwamishinan.

Fatima wadda ta saudaukar da albashinta na shekaru hudun da tayi aiki ga shirin samar da lafiya na jihar ta ce akwai yiwuwar za ta amince ta cigaba da aiki da gwamnati idan sabon gwamna Fintiri ya bukaci ta cigaba da aiki da gwamnatinsa.

"Zan yi tunani a kan hakan ko ba dan komai ba saboda al'ummar Adamawa," inji ta.

NAN ta ruwaito cewa wasu daga cikin kwamishinonin gwamna Bindow sunyi murabus sun koma jam'iyyar APC yayin da mahaifinta Atiku ya sauya sheka daga APC zuwa PDP.

Amma Fatima ta cigaba da aikinta na fannin lafiya a jihar inda ta ce harkar lafiya ba siyasa bane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel