Sabon gwamna ya kara mata ta 3 kwana daya bayan darewarsa madafan iko

Sabon gwamna ya kara mata ta 3 kwana daya bayan darewarsa madafan iko

Kimanin kwana daya tal da darewarsa kujerar gwamna, sabon gwamnan jahar Yobe Mai Mala Buni ya kara aure, inda ya auri diyar tsohon gwamnan jahar Yobe, Ibrahim Gaidam daya mika masa mulki a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito sunan amaryar Ummi Adama Gaidam, kuma a yanzu haka tana karatun digiri a wata jami’a dake kasar Saudi Arabia, sai Ummi zata shiga gidan sabon gwamnan ne a matsayin mace ta uku.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da babban Malami a Katsina

Sabon gwamna ya kara mata ta 3 kwana daya bayan darewarsa madafan iko

Mala da Gaidam
Source: UGC

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Gwamna Buni da kansa ne ya fara neman auren Ummi ba tare da sanin mahaifnta ba, kuma yayi haka ne domin kara karfafa dankon zumunci dana siyasa dake tsakaninsa da tsohon gwamna Gaidam.

An daura wannan aure ne a gidan Gaidam dake unguwar Sabon Fegi, cikin garin Damaturu na jahar Yobe a ranar Alhamis, 30 ga watan Mayu a gaban wasu zababbun yan uwa da abokan arziki da aka gayyata cikin sirri.

A iya cewa Ummi ta cika yar gata, sakamakon angonta ya kasance tsohon sakataren jam’iyya mai mulki jam’iyyar APC, wanda a yanzu ya zama gwamna, yayin da mahaifinta kuma tsohon gwamna ne daya kwashe shekaru 10 yana mulki a Yobe, sa’annan a yanzu ya lashe zaben zama Sanata dan majalisar dattawa.

A ranar Laraba 29 ga watan Mayu ne Gwamna Mai Mala Buni ya karbi rantsuwar kama ragamar mulkin jahar Yobe a hannun Alkalin Alkalan jahar, Mai sharia Garba Na Baruma.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel