Bayan kwanaki takwas da dawo wa, shugaban kasa Buhari ya koma kasar Saudiya

Bayan kwanaki takwas da dawo wa, shugaban kasa Buhari ya koma kasar Saudiya

Bayan kwanaki takwas da dawo wa daga kasar Saudiya inda ya gudanar da aikin Umara, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tashi daga birnin Abuja a ranar Alhamis zuwa birnin Jedda na kasar Saudiya.

Kamar yadda mai magana da yawun shugaban kasa Mallam Garba Shehu ya bayyana a ranar Laraba, shugaban kasa Buhari zai ziyarci kasar Saudiya domin halartar taron kungiyar hadin kan musulunci ta duniya OIC, da za a gudanar a birnin Makkah.

Bayan kwanaki takwas da dawo wa, shugaban kasa Buhari ya koma kasar Saudiya

Bayan kwanaki takwas da dawo wa, shugaban kasa Buhari ya koma kasar Saudiya
Source: UGC

Taron karo na 14 wanda Sarkin Saudiya Salman Bin Abdulaziz Al Saud zai kasance mai masaukin baki, zai gudana a ranar Juma'a 31, ga watan Mayun 2019 inda shugabannin kasashen kungiyar OIC za su halarta.

Ana sa ran shugaban kasa Buhari zai gabatar da jawaban a babban taron kan maudu'in muhimmancin hadin kai a tsakanin kasashen kungiyar OIC na yiwa kalubalen da kowanen su ke fuskanta rubdugu musamman ta'addanci da kuma ra'ayin rikau.

Shugaban kasa Buhari da ake sa ran dawowar sa gida Najeriya a ranar 2 ga watan Yunin 2019 zai yi tattaki da babbar tawaga da ta hadar da; gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar, Gboyega Oyetola na jihar Osun da kuma gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello.

KARANTA KUMA: Tsohon Ministan Sadarwa ya nemi Oshiomhole ya yi murabus

Sauran 'yan tawagar shugaban kasa Buhari sun hadar da babban sakataren ma'aikatar harkokin kasashen ketare Mustapha Suleiman, shugaban hukumar leken asiri Ahmed Rufa'i Abubakar, shugaban ma'aikatar NITDA Isa Ali Pantami da kuma shugaban hukumar jin dadin Alhazai, Abdullahi Mukhtar.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari zai kasance shugaban Najeriya na uku da suka halarci babban taron na OIC bayan tsaffin shugabannin kasar nan Marigayi Umaru Yar Adu'a da kuma Goodluck Ebele Jonathan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel