Bello Matawalle ya rugurguza Majalisar zartarwar Jihar Zamfara

Bello Matawalle ya rugurguza Majalisar zartarwar Jihar Zamfara

Mun samu labari cewa Dr. Bello Muhammad Matawallen Muradun ya dauki matakan farko bayan an rantsar da shi kan kujerar gwamnan jihar Zamfara a jiya Laraba 29 ga Watan Mayun nan.

Kamar yadda labari ya zo mana daga jihar Zamfara, sabon gwamna Bello Muhammad, ya sallami daukacin wadanda gwamna Abdulaziz Yari ya dauka aiki a lokacin yana kan kujear mulki.

Daga rantsar da gwamnan ne ya fito ya bayyana cewa ya ruguza majalisar zartarwar jihar mai dauke da manyan kwamishinonin jihar Zamfara. Wani Sakataren-din-din na jihar ya bayyana wannan.

A sanarwar da ta fito daga bakin Ibrahim Sulaiman Anka (Wamban Anka), yace gwamnatin Zamfara ta sauke duk wasu masu rike da mukaman siyasa a jihar daga kan kujerursu a halin yanzu.

KU KARANTA: Gwamnan Yobe yayi nadin mukami a ranar da ya hau kan mulki

Bello Matawalle ya rugurguza Majalisar zartarwar Jihar Zamfara
Gwamnan Jihar Zamfara Dr. Bello Muhammad Matawalle
Asali: Facebook

Bugu da kari, wannan gwamnati da aka nada yanzu, ta kori duk wasu Hadiman gwamnan jihar da sauran ‘yan siyasa, sannan kuma ta rushe kowane irin kwamiti da ke aiki a jihar kafin yanzu.

Ba nan kurum abin ya tsaya ba, domin gwamna Bello Mutawalle ya sauke daukacin majalisun da ke kula da hukumomin jihar, illa majalisar da ke lura da ma'aikatan gwamnati da na bangaren shari’a.

Gwamna Bello Mutawalle ya kuma ruguza majalisar da aka kafa domin lura da majalisar dokoki da kuma hukumar zaben jihar Zamfara. Wannan mataki da aka dauka ya fara ne tun jiya Laraba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel