Hotuna: Wasu kalaman soyayya da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yiwa matarsa, jim kadan bayan rantsar dasu

Hotuna: Wasu kalaman soyayya da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yiwa matarsa, jim kadan bayan rantsar dasu

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo shima ya ce baza a barshi a baya ba a fannin soyayya, inda ya fita shafin sada zumunta na Twitter ya dinga koda matarsa akan irin kokarin da tayi masa wurin karfafa masa gwiwa a lokacin wa'adinsu na farko

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo yayi wasu kalamai na soyayya akan kyakkyawar matarshi, Dolapo Osinbajo, da irin jajircewar da ta yi wurin ganin sun ciyar da kasar nan gaba a wa'adinsu na farko.

Yayin da suke kokarin shiga sabuwar gwamnati a karo na biyu, a jiya 29 ga watan Mayu lokacin da ake rantsar su, shi da shugaban kasa Muhammadu Buhari, mataimakin shugaban kasar ya sanya wani shi da matarsa a shafinsa na Twitter inda yake gode mata da irin karfin gwiwar da ta dinga bashi a lokacin gwamnatinsu ta farko.

Hotuna: Wasu kalaman soyayya da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yiwa matarsa, jim kadan bayan rantsar dasu
Hotuna: Wasu kalaman soyayya da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yiwa matarsa, jim kadan bayan rantsar dasu
Asali: Facebook

Ya kara da cewa a wannan karon ma a shirye yake su shiga sabuwar gwamnati a karo na biyu mutukar kyakkyawar matar tashi tana tare dashi.

KU KARANTA: Wurare hudu da shugaba Buhari zai bai wa muhimmanci a wannan karon - Sani Zoro

Ga abinda mataimakin shugaban kasar ya rubuta a shafin nasa na Twitter:

Hotuna: Wasu kalaman soyayya da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yiwa matarsa, jim kadan bayan rantsar dasu
Hotuna: Wasu kalaman soyayya da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yiwa matarsa, jim kadan bayan rantsar dasu
Asali: Facebook

Jiya 29 ga watan Mayu ne dai aka rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo a karo na biyu a filin wasa na Eagle Square dake babban birnin tarayya Abuja.

Hakazalika an rantsar da sababbin gwamnoni kimanin 29 a fadin jihohin kasar nan a jiyan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel