Farawa da iyawa: Sabon gwamnan jihar Zamfara zai mayar da ma'aikata 1,400 da aka kora bakin aikinsu

Farawa da iyawa: Sabon gwamnan jihar Zamfara zai mayar da ma'aikata 1,400 da aka kora bakin aikinsu

- Jim kadan bayan an rantsar dashi a matsayin gwamnan jihar Zamfara, sabon gwamnan yayi alkawarin mayar da ma'aikata 1,400 da aka kora daga aiki bakin aikinsu

- Ma'aikatan 1,400 sun biyo bashin albashi na watanni 60, maimakon a biyasu albashin nasu sai aka kore su a aiki

Sabuwar gwamnatin jihar Zamfara ta sha alwashin mayar da ma'aikata 1,400, wadanda tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari ya kora bakin aikin su.

Gwamnan jihar Muhammad Bello Matawallen Maradun shine ya bayyana hakan jiya Laraba a garin Gusau, yayin da yake yin bayani lokacin da ake rantsar dashi a matsayin sabon gwamnan jihar, shi da mataimakinsa Mahdi Aliyu Gusau.

Farawa da iyawa: Sabon gwamnan jihar Zamfara zai mayar da ma'aikata 1,400 da aka kora bakin aikinsu

Farawa da iyawa: Sabon gwamnan jihar Zamfara zai mayar da ma'aikata 1,400 da aka kora bakin aikinsu
Source: Facebook

Ma'aikatan na bin bashin albashi na watanni 60, amma sai aka kore su daga bakin aikinsu ba tare da an biya su albashin nasu ba, sabon gwamnan jihar Matawallen Maradun yace zai mayar da ma'aikatan bakin aikinsu domin cigaba da gabatar da ayyukansu kamar yadda suka saba.

KU KARANTA: Yadda bakin talauci ke tilasta 'yan mata shiga harkar karuwanci a jihohin kasar nan

"Saboda haka, wannan gwamnati za ta kafa kwamitin da za ta tantance su sannan zamu mayar da kowannen su bakin aikinsa, sai dai kawai wadanda suka samu sabon aikin yi," in ji sabon gwamnan.

A jiya Laraba ne aka yi bikin rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan guda 29 a fadin kasar nan, ciki kuwa hadda sabon gwamnan jihar Zamfara, wanda kotu ta bashi kujerar gwamnan jihar a makon da ya gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel