Na fi gwamnatin Buhari amfani a wurin 'yan Najeriya - Buba Galadima

Na fi gwamnatin Buhari amfani a wurin 'yan Najeriya - Buba Galadima

Kakakin yakin zaben Atiku Abubakar kuma tsohon aminin Shugaba Muhammadu Buhari Injiniya Buba Galadima ya ce ya fi yi wa talakawa da al'ummar Najeriya alheri a kan gwamnatin Najeriya.

Galadima ya yi wannan jawabin ne cikin wata hira da akayi da shi a BBC inda ya ke bayyana ra'ayinsa kan yadda mulkin shugaba Muhammadu Buhari karo na biyu za ta kasance.

Ya kara da cewa Buhari ba zai iya tabbuka wani abin azo a gani ba saboda baya daukan shawarwari kuma baya iya daukan mataki a kan 'yan fadarsa ko da an same su da laifuka.

Na fi gwamnatin Buhari amfani a wurin 'yan Najeriya - Buba Galadima
Na fi gwamnatin Buhari amfani a wurin 'yan Najeriya - Buba Galadima
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Ganduje ya mayar da wasu manyan kusoshin gwamnatinsa kan mukamansu

"Ba zai iya ba. Mutumin da bai iya sauya wa minista mukami ba ko da ya saci Najeriya ne, ko Buharin da kansa ya sata. Yaushe zai sauya wani ya kawo wani mutum?.

"Na kusa da shi sun riga sun kange shi, bai iya jin gaskiya. Yanzu wannan maganar sai a ce masa Buba makiyinka ne. Maimakon a ce masa Buba masoyinka ne, sauke kayanka baya zama sauke mu raba," a cewar Buba.

Da ya ke martani kan wadanda suke ikirarin cewa yan sukar gwamnatin Buhari ne saboda ba a bashi mukami ba, Ya kada baki ya ce taimakon al'umma ya ke yi saboda yana sa gwamnati aikata wasu abubuwan da ba tayi shirin yi ba.

Ya cigaba da cewa demokradiya ba za ta inganta ba muddin babu 'yan hamayya da za su rika yiwa gwamnati gyara da nasiha inda ya ce 'hannu daya baya tafi' hakan na nufin hammaya abu ne mai amfani a kowanne demokradiyya.

Buba Galadima dai ya dade yana suka gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da jam'iyyar APC tun lokacin da ya ware daga jam'iyyar saboda rashin jituwa da aka samu tsakaninsa da uwar jam'iyyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel