Daga Obasanjo zuwa Buhari: Abu 4 da ake tuna wa a gwamnatin kowannen su

Daga Obasanjo zuwa Buhari: Abu 4 da ake tuna wa a gwamnatin kowannen su

A yayinda ranar sake rantsar da zababben shugaban kasar Najeriya a mulkin dimokradiyya ta sake dawowa, masu nazarin siyasa da al'amuran gwamnati sun yi duba cikin wasu muhimman abubuwa da shugabannin Najeriya da aka zaba daga shekarar 1999 zuwa yanzu suka yi a gwamnatinsu, wadanda kuma yawancin jama'a ke tuna wa idan ana maganar mulkin su.

Olusegun Obasanjo (1999 zuwa 2007)

1. Shine ya kafa hukumomin yakin cin hanci guda biyu; EFCC da ICPC sannan ya kara wa hukumar da'ar ma'aikata karfi domin yakar cin hanci. A loakcinsa ne aka fara daure 'yan siyasa da jami'an gwamnati ko ma'aikata saboda laifin hanci, misali Bode George da Tafa Balogun

2. Shine ya shiga ya fita har aka yafe wa Najeriya bashin dala biliyan $18 na Paris da Landan kulob

3. Ya kawo siyasar 'ko a mutu, ko a rayu' a kokarinsa na kafa yaransa na siyasa a kujeru daban-daban. Ya gudanar da zabukan masu muni dake cike da magudi da murdiya.

4. Ya yi amfani da ofishinsa wajen sayar wa da kansa manyan kadarorin gwamnati irin su Otal din Transcorp tare da bawa kansa manyan kwangiloli.

5. Ya so ya murda kundin tsarin mulki domin samun damar yin tazarce a karo na uku bayan ya lashe wa'adin zangonsa biyu kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanada.

Umaru Musa Yar'adu (2007 zuwa 2010)

1. Shine shugaban kasar Najeriya na farko da ya fara bayyana dukiyar sa kafin ya hau mulki. Sannan ya amsa cewar an tafka kura-kurai a zaben da ya lashe a shekarar 2007.

2. Shine ya sakar wa jihar Legas biliyan N10, kudin kananan hukumominsu da Obasanjo ya hana su saboda dalilan siyasa.

3. Mutane basa manta yadda Yar'adua ya ki hakura ya mika mulkin kasa ga mataimakinsa, Goodluck Jonathan, bayan rashin lafiyarsa ta tsananta.

4. Ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo karshen aiyukan tsagerun yankin Neja-Delta ta hanyar kafa hukumar kula da yankin tare da tura tubabbun tsageru zuwa kasashen duniya domin koyon sana'o'i

Goodluck Jonathan (2010 zuwa 2015)

1. Jama'a basa manta yadda Jonathan ya funfurus tare da kin bayyana kadarar sa duk da irin nacin da 'yan Najeriya suka nuna a kan bukatar ya yi hakan.

2. Bayan an rantsar da shi, Jonathan ya yafe wa wasu tsofin gwamnoni; Dierey Alameigha da James Ibori, da aka yanke wa hukunci bayan samun su da laifin wawurar dukiyar talakawansu. Kazalika, jama'a basa manta yadda ya hana a binciki wasu ministocinsa mata guda biyu; Stella Oduah da Diezani Allison Madueke, bisa zarginsu da tafka badakala a ma'aikatun da suke jagoranta. Daga bisani ya cire Stella daga mukamin minista ba tare da kuma an bincike ta.

3. Jonathan ya gaji dalar Amurka biliyan $60 a asusun Najeriya a bankin duniya amma ya lalata shi har ya koma dalar Amurka biliyan $40 a cikin shekaru biyar. Abinda ya kara bata wa 'yan Najeriya rai shine yadda Jonathan ya gaza kara ko sisi a asusun Najeriya duk da hauhawar farashin danyen man fetur da aka samu a duniya lokacin da yake mulki, hasali ma saida ya taba wadanda ya samu an tara a cikin asusun.

4. A lokacin mulkinsa ne matsalar Boko Haram ta munana a arewacin Najeriya, lamarin da ya jawo masa rasa goyon bayan jama'ar yankin a zaben da aka kayar da shi a shekarar 2015.

5. Bayan an sanar da sakamakon zabe ya kira Buhari ya taya shi murna tare da yi masa fatan alheri.

Muhammadu Buhari ( 2015 zuwa 2019)

1. Gwamnatinsa ce ta kaddamar da tsarin asusun bai daya (TSA) tare da tilasta dukkan hukumomi, ma'aikatun gwamnati rungumar tsarin amfani da TSA.

2. Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arzikin kasa (EFCC) ta kara tsanani wajen bincike tare da gurfanar da manyan siyasa a gaban kotu bisa tuhumarsu da cin hanci. Saidai, wasu sun yi korafin cewar ana nuna son kai wajen zabar wadanda za a bincika da laifukan cin hanci.

3. An samu bullar matsalolin tsaro da suka hada da garkuwa da mutane, fashi da makami, satar shanu da rikicin makiya da manoma a zangon mulkinsa na farko. Rashin tsaron ya fi tabarbarewa a yankin arewacin Najeriya.

4. An zarge shi da yawan ficewa daga Najeriya a zango na farko na mulkinsa. Wata kididdiga ta bayyana cewar ya shafe kwanki 360 (adadin kwanaki shekara) ba a cikin Najeriya ba a shekaru na mulkinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel