Yanzu Yanzu: El-Rufai ya bayar da motarshi don a kwashi wasu da suka yi hatsari zuwa Asibiti (hotuna)

Yanzu Yanzu: El-Rufai ya bayar da motarshi don a kwashi wasu da suka yi hatsari zuwa Asibiti (hotuna)

- Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya tsayar da tawagarsa yayinda hatsari ya cika da wasu a hanyarsa ta dawowa daga wani taro

- El-Rufai ya bayar da motarsa domin a kwashi wadanda suka jikkata zuwa asibiti

- Hatsarin dai ya afku ne a tsakanin wata mota kirar Bus da Keke Napep a inda nan take motar ta kama da wuta

Labari da ke zuwa mana ya nuna cewa gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai a hanyarsa ta dawowa daga wani waje, sai ya ci karo da wani mumunan hatsari tsakanin wata mota kirar Bus da Keke Napep a inda nan take motar ta kama da wuta.

Hakan yasa gwamnan ya tsaya tare da tawagarsa sannan ya bayar da motarsa aka kwashi wadanda suka jikkata a hatsarin zuwa asibiti.

Yanzu Yanzu: El-Rufai ya bayar da motarshi don a kwashi wasu da suka yi hatsari zuwa Asibiti (hotuna)

Yanzu Yanzu: El-Rufai ya bayar da motarshi don a kwashi wasu da suka yi hatsari zuwa Asibiti
Source: Facebook

Majiyarmu ta ruwaito cewa Gwamna Elrufai da mataimakinshi Bala Bantex da Hadiza Balarabe da kuma matanshi Biyu, Hadiza Elrufai da Aisha Ummi Elrufai suna fitowa ne daga "State House" dake hanyar Kawo bayan sun halarci bikin nuna hotunan ayyukan Gwamnan a zangon mulkinsa na farko.

KU KARANTA KUMA: An samu nasarar kubutar da matar dan majalisa da 'ya'yansa guda biyu da aka sace a jihar Gombe

Yanzu Yanzu: El-Rufai ya bayar da motarshi don a kwashi wasu da suka yi hatsari zuwa Asibiti (hotuna)

Yanzu Yanzu: El-Rufai ya bayar da motarshi don a kwashi wasu da suka yi hatsari zuwa Asibiti
Source: Facebook

Lamarin ya auku ne a daidai "Signboard" dab da ginin "state house" din da Gwamnan ya fito taro a yau Laraba, 28 ga watan Mayu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel