Gidan aro: Almakura ya mika wa Sule makullen gidan gwamnatin Nasarawa

Gidan aro: Almakura ya mika wa Sule makullen gidan gwamnatin Nasarawa

Gwamnan jihar Nasarawa mai barin gado, Alhaji Umaru Tanko Al-Makura ya mika makullan gidan gwamnati, Lafia ga gwamna mai jiran gado, Injiniya Abdullahi Sule.

Almakura ya mika makullan ne a wani taron da aka gudanar wanda ya samu halartan ma’aikatun gidan gwamnati.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gwamna mai barin gadon ya bar gidan gwamnati bayan an kammala taron tare da hadimansa bayan iyalansa sun bar gidan kafin taron.

Gidan aro: Almakura ya mika wa Sule makullen gidan gwamnatin Nasarawa

Gidan aro: Almakura ya mika wa Sule makullen gidan gwamnatin Nasarawa
Source: Twitter

A jawabinsa, Gwamna Al-Makura yace, “Mun shafe sa’o’i muna ganawa da wanda zai maye gurbina a lokacin mika gwamnati; a halin yanzu a shirye yake saboda ya ga bayanai da kuma lissafi akan ayyukan da aka kaddamar da kuma yanda aka gudanar da mulki a shekarun da suka gabata.

Har ila yau yayin da yake magana, gwamna mai jiran gadon, Injiniya Abdullahi Suke yace “muna shaida damar daya daga cikin mafi natsatsun mutane tare da shugabanci mai inganci”.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta aika sammaci ga kwamishinan yan sandan Niger kan rashin kama tsohon gwamna Aliyu da Nasko

“Na sanya idanu sosai a aikin Gwamna Al-Makura; ba zai fita da komai daga gidan gwamnati ba. Ina yiwa mutanen Nasarawa alkawarin cewa zan inganta shi fiye da yadda na same shi. Ina yi masa tare da iyalansa addu’an samun kariyar Allah.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel