Gwamna Bello na jihar Neja ya rushe majalisarsa

Gwamna Bello na jihar Neja ya rushe majalisarsa

- Gwamnan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello ya dakatar da dukkanin 'yan majalisar fadarsa

- Dakatarwar na su zai fara aiki ne daga yau Larabar 28 ga watan Mayu

- Hakan na zuwa ne yan kwana daya kafin rantsar da sabbin gwamnonin jihohi a fadin kasar da za a yi a ranar 29 ga watan Mayu

Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello ya rushe majalisar jihar a daren Litinin inda ya umurci kwamishinoninsa su mika dukkan ayyukan da ke hannunsu ga manyan Sakatarorin ma'aikatun gwamnatin anan take.

Ya kuma bukaci sauran masu rike da mukamman siyasa su bi sahun kwamishinonin na mika ayyukansu ga manyan ma'aikata na hukumomi da ma'aikatunsu.

Gwamna Bello na jihar Neja ya rushe majalisarsa

Gwamna Bello na jihar Neja ya rushe majalisarsa
Source: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sunyi garkuwa da mai shirya fina-finai, sun nemi N10m

A cewar sanarwar da hadimin gwamnan, Malam Jibrin Ndache ya fitar, ya ce gwamna Bello ya dauki matakin ne yayin taron da aka gudanar da sa'o'i.

Sanarwar ta ce Gwamna Bello ya bukaci 'yan majalisar sa su kammala mika ayyukansu kafin karfe 12 na daren Talata.

Gwamnan ya mika godiyarsa ga 'yan majalisarsa bisa ayyukan da suka yiwa jihar a lokacin da ake bukarsu.

"Ina son mika godiya ta musamman gare ku bisa ayyukan da kuka yiwa jihar mu. Kun bayar da muhimmiyar gudunmawa wurin cigaban al'ummar mu na tsawon shekaru hudu da suka gabata. Kun bayar da gudunmawa wurin samun nasarar 'Restoration Agenda'."

"Ina muku fatan alheri a duk wani aikin da za kuyi a gaba kuma ina fatan za ku cigaba da aiki domin cigaban jihar mu. Ina godiya bisa gudunmawar da kuka bayar," inji sanarwar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit Newspaper

Online view pixel