Bayan shekaru fiye da 20 Najeriya ta cika alkawarin da tayi wa Westerhof
Labari ya zo gare mu cewa, shekaru kusan 25 da yin alkawarin ba tsohon kocin ‘yan wasan kwallon kafan Najeriya, Clemens Westerhof, gwamnati ta cika wannan alkawari da tayi a makon nan.
A shekarar 1994 ne wannan babban Koci, Clemens Westerhof, ya taimakawa Najeriya ta lashe gasar cin kofin Nahiyar Afrika watau AFCON, sannan kuma Super Eagles ta samu zuwa gasar Duniya.
Clemens Westerhof wanda ya kasance kwararren mai horaswa, shi ya fara kai Najeriya zuwa ga wasan cin kofin Duniya a tarihi. Wannan ne ya sa aka yi masa alkawarin gida a wancan lokaci.
A karkashinsa ne ‘Yan wasan Super Eagles na Najeriya su ka je gasar cin kofin Duniya da aka yi a kasar Amurka a 1994. Sai dai bayan shekaru 25, Najeriya ba ta cika wannan alkawari da tayi ba.
KU KARANTA: Sanatar Najeriya ta sha da kyar a hannun wasu 'Yan daba
Ministan gidaje da hanyoyi da harkar wuta na Najeriya, Babatude Fashola shi ya cika wannan alkawari a madadin gwamnatin Najeriya a Ranar Litinin dinnan 27 ga watan Mayun nan na 2019.
“Gwamnatin kasar ta ba tsohon koci (Clemens Westerhof) wannan gida ne domin inganta harkar wasanni wanda ke hada kabilu dabam-dabam.” Inji Ministan kasar watau Tunde Fashola.
Ministan ya karasa bayaninsa da cewa:
“Wannan abu da aka yi, zai taimaka kwarai wajen karfafawa sauran ‘yan wasan da ake da su na Maza da Mata gwiwa…”
Westerhof mutumin kasar Holland ne wanda ya horas da kasashen Afrika daga karshen shekarun 1980s har zuwa cikin 1990s. Yanzu tsufa ya kama Kocin inda yake dosan shekaru 80 a Duniya.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng