Ku cigaba da yi ma Sarki Sunusi biyayya – Masarautar Kano ga hakimai

Ku cigaba da yi ma Sarki Sunusi biyayya – Masarautar Kano ga hakimai

Fadar mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ta yi kira ga kafatanin hakimai da dagatan dake kananan hukumomin jahar Kano dasu cigaba da yi masa biyayya a matsayinsa na Sarki guda daya tilo a jahar Kano gabaki dayanta.

An bayyana haka ne ta cikin wata sanarwa data fito daga fadar masarautar Kano dake dauke da sa hannun guda daga cikin manyan yan fada, Awaisu Abbas Sunusi, sanarwar data bukaci masu rike da sarautaun gargajiya dasu cigaba da karbar umarni daga Sarki Sunusi.

KU KARANTA: Ke duniya! Kalli Malamin dake yin luwadi da almajiransa, kuma yana bada hayarsu a Sakkwato

Ku cigaba da yi ma Sarki Sunusi biyayya – Masarautar Kano ga hakimai

Sarkin Kano
Source: UGC

Sanarwar fadar ta bayyana cewa ya zama wajibi tayi wannan kira da babban murya duba da cewa batun samar da sabbin sarakuna masu daraja ta daya a jahar Kano na gaban kotu, kuma kotu ta umarci gwamnati ta dakata.

Haka zalika fadar tayi kira ga hakimai da dagatai da kada su ji tsoron yin biyayya ga masarautar Kano domin tana da kwararrun lauyoyi data dauka da zasu kare musu hakkinsu, daga karshe fadar tayi kira garesu dasu dage da addu’o’I don ganin jarabawar da masarautar ke fuskanta yazo karshe.

Idan za’a tuna Manyan hakiman fadar Sarkin Kano guda hudu wadanda hakkin zaben Sarki a masarautar Kano ya rataya a wuyansu sun nuna ma Ganduje yatsa game da raba masarautar Kano, inda suka garzaya gaban kotu domin kalubalantarsa.

Wadannan manyan hakiman sun hada da Madakin Kano Yusuf Nabahani, Makaman Kano Sarki Ibrahim, Sarkin Dawaki maituta, Bello Abubakar da kuma Sarkin Bai, Mukhtar Adnan hakimin Dambatta.

Manya daga cikin jerin lauyoyin da hakiman suka dauka haya sun hada da Lateef Fagbemi, AB Mahmoud, Adeniyi Akintola, Paul Usoro, Suraj Sa’eda, Hakeem Afolabi da Nassir Dangiri, dukkaninsu masu lambar girma ta SAN.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel