Kabiru Classic zai wakilci Yankin Anka da Mafara a Majalisar Tarayya

Kabiru Classic zai wakilci Yankin Anka da Mafara a Majalisar Tarayya

Mun samu labari cewa fitaccen Mawakin Hausan nan wanda ake kira Classic ya zama ‘dan majalisar tarayya mai jiran-gado a jihar Zamfara bayan hukuncin da kotun koli tayi a makon da ya gabata.

Kabiru Yahaya Classic yana cikin ‘yan takarar jam’iyyar adawa ta PDP da su samu kujerar majlisar tarayya a jihar Zamfara. Classic zai wakilci Mazabar sa ta Anka da kuma Talata Mafaran Zamfara.

Wannan Mawaki wanda yayi fice shi ne zai wakilci mutanen Mazabar Talata Mafara da kuma Anka a majalisar wakilai a 2019. Shi kan sa gwamna Abdulaziz Yari ya fito ne daga Talata Mafara.

Kamar yadda mu ka samu labari, jama’a sun yi farin ciki da nasarar da Mawakin ya samu bayan hukuncin kotu. Classic ya bayyana nasarar da ya samu da cewa lamarin Ubangiji ne ba komai ba.

KU KARANTA: PDP ta na hango nasarar Atiku bayan sakamon shari'ar Zamfara

Kabiru Classic zai wakilci Yankin Anka da Mafara a Majalisar Tarayya
Classic ya zama 'Dan majalisar Anka da Garin Talata Mafara
Asali: Facebook

Alhaji Kabiru Classic na PDP shi ne ya zo na biyu bayan Sharu Anka a zaben na 2019, amma ya samu kujerar Mazabarsa bayan kotu ta rusa duka kuri’un da jam’iyyar APC ta samu a zaben.

Kabiru Yahaya Classic yana cikin manyan ‘yan a-mutun PDP a Zamfara. Wani Bawan Allah da ke jihar ya bayyana mana cewa jama’a da dama sun dauka Mawakin ba zai kai labari ba.

Haka zalika kuma mun samu labari cewa wani daga cikin ‘Ya ‘yan Marigayi Sheikh Abubakar Gumi mai suna Suleiman Abubakar Gumi ya lashe kujerar ‘dan majalisar Gumi da Bukuyum a jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel