Kin yi magana ba tare da kina da ilimin SIP ba - Maryam Uwais ta mayar wa Aisha raddi

Kin yi magana ba tare da kina da ilimin SIP ba - Maryam Uwais ta mayar wa Aisha raddi

Maryam Uwais, babbar mai taimakawa shugaban kasa a kan shirin bayar da tallafi, ta kare gwamnatin tarayya a kan sukar shirin bayar da tallafi (SIP) da uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, tayi ranar Asabar da ta gabata.

Uwais ta bayyana cewar Aisha Buhari zata iya bin kwakwafi domin gano duk wani mai cin moriyar shirin bayar da tallafi da ace tana da bayanai a kan shirin SIP da take suka.

Da take magana a wani shirin gidan Talabijin na Channels, Maryam ta bayyana cewar 'yan Najeriya 190,000 ne shirin bayar da tallafin ke biya kowanne wata.

A ranar Asabar ne Aisha Buhari ta bayyana cewar shirin SIP ya gaza tabuka komai a arewacin Najeriya, tare da zargin Maryam Uwais, mai bawa shugaban kasa shawara a kan shirin bayar da tallafi, da rashin dacewa da mukamin da aka bata.

Uwargidan shugaban kasar ta bayyana hakan ne yayin wani taro da tayi da mata a fadar shugaban kasa, inda ta soki shirin bayar tallafi da Maryam Uwais ke jagoranta.

Aisha ta ce an fada mata cewar mata 30,000 daga jihar Adamawa zasu ci moriyar shirin bayar da tallafin amma hakan ta gaza yiwuwa.

Kin yi magana ba tare da kina da ilimin SIP ba - Maryam Uwais ta mayar wa Aisha raddi

Maryam Uwais
Source: Twitter

Da take magana a cikin shirin gidan Talabijin na kai tsaye, Maryam ta ce Aisha tayi magana ne ba tare da tana da ilimi ko bayanai a kan shirin SIP ba.

Ta ce yanzu haka kananan hukumomi 12 a jihar Adamawa na cin moriyar shirin bayar da tallafi, bayan kimanin matasa 11,000 da suka kammala karatun gaba da sakandire daga jihar dake cin moriyar shirin.

"Na tabbata da zata gudanar da bincike daga bayanan da muke da su, zata iya zakulo dukkan masu cin moriyar shirin.

DUBA WANNAN: Ba sharri muke yiwa gwamnatin Buhari ba, Aisha ta tabbatar da hakan - PDP

"Ba lallai ta sadu da mutanen dake cin moriyar shirin ba, amma mutane daga kanan hukumomi 12 dake jihar Adamawa na amfanar shirin. Kazalika muna gudanar da shirin bayar da tallafi a kananan hukumomin 12. Akwai kimanin mutane 290,000 dake cin moriyar shirin SIP kai tsaye daga jihar Adamawa," a cewar Maryam.

Maryam ta kara da cewa a yanzu haka makarantun firamare fiye da 1,000 na amfanar shirin ciyar wa daga cikin kudaden da gwamnati ta ware wa shirin SIP.

"Muna da matasa da suka kammala karatu fiye da 11,000 da suke cin moriyar shirin SIP daga jihar ta. Muna da wasu matasan dake cin moriyar shirin su 440, mun fara shirin ciyar da dalibai a watan Oktoba na shekarar 2018, wanda yanzu haka makarantun firamare 1,054 a jihar ke amfana," a cewar ta.

Maryam ta bayyana cewar shirin zai fi haka taka rawar gani da a ce kudin da yake samu sun fi haka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel