Murnar cika shekaru 88: Buhari ya jinjina ma Aminu Alhassan Dantata

Murnar cika shekaru 88: Buhari ya jinjina ma Aminu Alhassan Dantata

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjina ma mashahurin attajiri Alhaji Aminu Dantata yayin daya cika shekaru tamanin da takwas, 88 a rayuwa, tare da yabawa da kyawawan dabi’unsa kamar yadda ya bayyana.

Legit.ng ta ruwaito shugaba Buhari ya bayyana haka ne ta bakin kaakakinsa, Malam Garba Shehu, wanda yace Dantata ya samar da wani tsarin taimaka ma matasa da dama wajen a fannin kasuwanci ta hanyar basu jari tare da habbaka kasuwancinsu.

Murnar cika shekaru 88: Buhari ya jinjina ma Aminu Alhassan Dantata

Murnar cika shekaru 88: Buhari ya jinjina ma Aminu Alhassan Dantata
Source: Facebook

KU KARANTA: Kowa ya debo da zafi: Matashin da yayi wanka a cikin kwata saboda Buhari yayi nadama

“Dantata na sane da cewa idan har jama’a basu bayar da goyon baya ga neman ilimi da kasuwanci ba, babu yadda za ayi kasar ta samu biyan bukata ta wajen habbaka tattalin arzikinta ba, balle kuma tayi gogayya da sauran kasashen duniya.

“Dantata daga cikin mutanen da suka dabbaka tubalin cigaban jahar Kano ta hanyar samar da shugabanci nagari, don haka nake fatan Allah Ya kara masa tsawon rai tare da shekaru masu albarka, Amin.” Inji Buhari.

Murnar cika shekaru 88: Buhari ya jinjina ma Aminu Alhassan Dantata

Murnar cika shekaru 88: Buhari ya jinjina ma Aminu Alhassan Dantata
Source: Facebook

A shekarar 1931 aka haifi Aminu Dogo, shine na goma sha biyar a cikin yaran Alhassan Dantata su goma sha bakwai, yayi karatun firamari a makarantar gwamnati ta Dala daga shekarar 1938 – 1945, a shekarar 1948 yayi aure, kuma ya shiga harkar kasuwanci ganga ganga.

Ga wadanda basu sani ba, Aminu Dogo Dantata kawu yake ga attajirin da yafi kudi a kafatanin nahiyar Afirka, Aliko Dangote, sakamakon mahafiyar Dangote, Mariya Dantata kanwarsa ce, mai karatu ya iya cewa danginsu sun gaji arziki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel