Mayakan Boko Haram sun kashe sojoji 25 a wani harin kwanton bauna

Mayakan Boko Haram sun kashe sojoji 25 a wani harin kwanton bauna

Jaridar The Cable ta wallafa wani rahoto dake cewa mayakan kungiyar Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya 25 da dumbin farar hula a wani harin kwanton bauna da suka kaddamar a jihar Borno.

Rahotan ya bayyana cewar mayakan kungiyar sun kai wa dakarun sojin harin kwanton bauna da safiyar ranar Asabar yayin da suke kokarin kwashe al'ummar wasu kauyuka a jihar.

Mayakan sun bude wuta a tawagar motoci kusan 50 da sojoji da fararen hula da aka debo daga kauyukan ke ciki.

"Sun kewaye motocin dake dauke da sojojin da fararen hula sannan sun bude musu wuta.

"Sun yi musayar wuta na dan wani lokaci kafin daga bisani mayakan su samu galaba a kan sojojin," kamar yadda wani mamba na kungiyar 'sa kai' da aka fi kira 'civilian JTF' ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Mayakan Boko Haram sun kashe sojoji 25 a wani harin kwanton bauna

Mayakan Boko Haram sun kashe sojoji 25 a wani harin kwanton bauna
Source: Twitter

Ko a ranar Laraba sai da mayakan kungiyar ta Boko Haram suka saki wani faifan bidiyo dake nuna wasu sojoji da suka kama a filin daga a yankin arewa maso gabas.

Mayakan sun yi bajakolin sojojin da suka kama tare da saka su fadin sunayen su da lambar su ta aiki da kuma rundunar da suke aiki tare da ita.

DUBA WANNAN: Abinda yasa muke samun nasara a yaki da 'yan bindiga a Sokoto - Kwamandan sojoji

Dakarun rundunar soji da jami'an rundunar 'yan sanda da mayakan suka yi bajakolin su, sun bayyana wuraren da aka kama su.

Rundunar soji tayi rashin dakaru da dama a sabbin hare-hare da mayakan kungiyar Boko Haram ke kai wa sansanin soji a 'yan kwanakin nan.

A ranar uku ga watan Mayu ne kungiyar IS tayi ikirarin cewar ta kashe sojojin Najeriya 10 a wani hari da ta kai a wani barikin soji dake Magumeri a jihar Borno.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel