APC ta nada sabon sakataren jam'iyya na kasa

APC ta nada sabon sakataren jam'iyya na kasa

Kwamitin gudanarwa na uwar jam'iyyar APC ya amince da nadin Victor Giadom a matsayin sabon mukaddashin sakataren jam'iyyar na kasa.

An nada Giadom ne domin ya maye gurbin tsohon sakataren jam'iyyar, Mai Mala Buni, wanda yanzu shine zababben gwamnan jihar Yobe.

Sanarwar da sakataren yada labaran jam'iyyar APC, Lanre Issa-Onilu, ya fitar, ta ce Mista Giadom zai kasance sakatare na riko kwarya har zuwa lokacin da jihar Yobe zata fitar da da wanda zai gaji Mista Buni a matsayin sakatare mai cikakken iko.

Kafin nada shi a matsayin sakatare na rikon kwarya, Mista Giadom, wanda dan asalin jihar Ribas ne, shine mataimakin sakataren jam'iyyar APC na kasa.

APC ta nada sabon sakataren jam'iyya na kasa

Shugaban jam'iyyar APC; Adams Oshiomhole
Source: Depositphotos

Mista Giadom ya taba zama shugaban karamar hukumar Gokana kafin daga bisani tsohon gwamnan jihar Ribas kuma ministan sufuri a yanzu, Rotimi Amaechi, ya nada shi a matsayin kwamishina daga shekarar 2011 zuwa 2015.

DUBA WANNAN: Rigar kowa: Yakubu Lame; dan takarar gwamna kuma jigo a APC ya mutu

Mista Giadom dan takarar mataimakin gwamna ga hamshakin dan kasuwa Tonye Cole, dan takarar APC da kotu ta soke takarar sa a jihar Ribas.

A wata sanarwar ta daban, kwamitin zartar wa na jam'iyyar APC ya taya gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Bagudu, murnar zama shugaban kungiyar gwamnonin da aka zaba a karkashin tutar jam'iyyar APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel