Rigar kowa: Yakubu Lame; dan takarar gwamna kuma jigo a APC ya mutu

Rigar kowa: Yakubu Lame; dan takarar gwamna kuma jigo a APC ya mutu

An sanar da mutuwar Dakta Ibrahim Yakubu Lame, jigo kuma dan takarar gwamnan jihar Bauchi a karkashin inuwar jam'iyyar APC a zaben shekarar 2019 da aka kammala.

Lame ya taba rike mukamin minista mai kula da harkokin rundunar 'yan sanda, sannan yana rike da sarautar 'Santurakin Bauchi'.

Dan siyasar ya rasu ne da samyin safiyar yau, Lahadi, a asibitin Nizamiye dake Abuja bayan ya sha fama da rashin lafiya.

An sallaci gawar sa da misalin karfe 10:00 a babban masallacin kasa dake Abuja, birnin tarayya.

Marigayi Dakta Ibrahim Yakubu Lame

Marigayi Dakta Ibrahim Yakubu Lame
Source: Facebook

Wani mai nazari a kan harkokin jama'a daga jihar Bauchi, Musa Azare, ya bayyana mutuwar a matsayin babban rashi ga kasa.

DUBA WANNAN: Aisha Buhari ta soki wata mai rike da mukamin siyasa da Buhari ya nada

An haifi Marigayi Lame, malami kuma dan siyasa, a shekarar 1953, sannan an zabe shi a matsayin sanata a shekarar 1992 lokacin jamhuriya ta uku. Toshon shugaban kasa Obasanjo ya nada shi a matsayin mai bashi shawara a shekarar 1999 kafin daga bisani tsohon shugaban kasa, Marigayi Umaru Musa Yar'adua, ya nada shi minista a shekarar 2008.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel