Manyan alkalai mata guda 8 da sunayen manyan 'yan siyasa da suke aure

Manyan alkalai mata guda 8 da sunayen manyan 'yan siyasa da suke aure

Majiyarmu ta binciko muku jerin manyan alkalai mata guda takwas da kuma sunayen mazajen su manyan 'yan siyasa na Najeriya da suke aure

Kwana biyu da suka wuce, alkalin kotun daukaka kara, Mai shari'a Zainab Bulkachuwa, ta ceto kanta daga rikicin karar zabe da take saurara, bayan da jam'iyyar PDP ta taso da zancen cewa mijinta dan jam'iyyar APC ne.

A yau majiyarmu Legit.ng za ta kawo muku jerin manyan alkalai mata da mazajensu wadanda suke manyan 'yan siyasa ne a kasar nan.

Manyan alkalai mata guda 8 da sunayen manyan 'yan siyasa da suke aure

Manyan alkalai mata guda 8 da sunayen manyan 'yan siyasa da suke aure
Source: Facebook

1. Mary Odili

Mary Odili ita ma wata shahararriyar alkali ce, matar tsohon gwamnan jihar Rivers Dr. Peter Odili, wanda ya fito takarar shugaban kasa a lokacin mulkin PDP.

2. Zainab Bulkachuwa

Zainab Bulkachuwa, ita ce shugabar kotun daukaka kara ta kasa. Tana auren zababben Sanatan APC na jihar Bauchi, Alhaji Adamu Bulkachuwa.

3. Fati Lami Abubakar

Fati matar tsohon shugaban mulkin soja ne, Gen Abdulsalami Abubakar (Rtd), wanda ya hau mulki bayan mutuwar tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha a shekarar 1998.

4. Binta Nyako

Binta Nyako ta na daya daga cikin manyan alkalai a Najeriya wacce sunanta ya karade kowanne lungu da sako na kasar nan. Binta Nyako ita ce matar tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako, wanda yayi mulki daga shekarar 2007 zuwa 2015.

KU KARANTA: An soke hawan sallah a jihar Katsina

5. Eberechi Wike

Eberechi Wike ita ce matar gwamnan jihar Rivers na yanzu, Cif Nyesom Wike.

6. Maryann Anenih

Maryann Anenih ita ce karama a cikin matayen Cif Anthony Anenih, tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa, wanda aka fi sani da sunan shi na siyasa da Mista Fix-It.

7. Chioma Nwosu-Iheme

Dr. Chioma Nwosu-Iheme alkalin kotun daukaka kara ce. Tayi karatu a bangaren shari'a har ta kai matsayin Farfesa, kuma ita ce mace ta farko da ta fara kaiwa wannan matsayin a Najeriya. Ita ce matar tsohon kwamishinan cigaban karkara, sannan kuma kwamishinan ilimi na jihar Imo.

8. Jumoke Pedro

Jumoke Pedro ita ce alkalin babbar kotun jihar Legas, tana auren tsohon mataimakin gwamnan jihar Legas Femi Pedro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel