Yanzu-yanzu: Jonathan ya samu sabon mukami
- Gwamnan jihar Bayelsa ya bai wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan mukami
- Seriake Dickson ya bai wa Jonathan mukamin mai ba shi shawara ta musamman a fannin ilimi
- Dickson ya roki Jonathan yayi amfani da wannan mukamin nashi wurin kawo cigaba a fannin
Jiya Juma'a ne 24 ga watan Mayu, gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson, ya bai wa tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan mukamin mai bada shawara ta musamman a fannin ilimi.
Da yake magana a wurin wani taro a garin Yenagoa, Dickson ya roki tsohon shugaban kasar yayi amfani da wannan mukami nashi wurin kawo cigaba a fannin ilimi a jihar.
Ya ce: "Bari na roki shugaban mu, tsohon shugaban kasa akan irin kokarin da yayi a fannin ilimi a lokacin yana gwamnan jihar nan, shine ginshikin farfado da fannin ilimi a jihar nan, hakanne ma yasa zan ba shi mukamin mai bada shawara ta musamman a fannin ilimi.
KU KARANTA: Kano: Ma'aikata sun shiga dar-dar yayin da Ganduje ya ciyo bashin dala miliyan 95
"Da wannan mukamin nashi, zai zauna a ma'aikatar ilimi ta jihar Bayelsa a matsayin tsohon malami, kuma kwararre da zai kawo cigaba a fannin."
Hakazalika, Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yaje birnin Johannesburg domin jagorantar harkar zaben a kasar Afirka ta kudu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana
Asali: Legit.ng