Kungiyar MOPPAN na shirin hana fim din soyayya a masana’antar Kannywood

Kungiyar MOPPAN na shirin hana fim din soyayya a masana’antar Kannywood

Kungiyar masu ruwa da tsaki na masana’antar shirya fina-finan Hausa (MOPPA) ta bayyana shirinta na yunkurin fara hana masu shirya wasanni yin fim din soyayya don su samu damay mayar da hankali ga wasu batutuwa na daban.

Shugaban kungiyar Kabiru Maikaba ne ya bayyana hakan a wata hira da yayi da shafin BBC, inda ya bayyana cewa kaso 80 cikin 100 na fina-finan Hausa duk na soyayya ne.

An tattaro inda yake cewa: "Me ya sa fina-finan soyayya kawai za mu rika yi bayan kuma akwai wasu bangarori da muke so a rika tabawa. Arewacin Najeriya na da dumbin tarihi, me ya sa ba za mu yi wasa game da hakan ba.

"Mun ce nan ba da jimawa ba, bayan babban zaben da za mu yi nan gaba kadan duk wani sabon fim da za a yi za mu bukaci sanin jigon labarinsa.

Kungiyar MOPPAN na shirin hana fim din soyayya a masana’antar Kannywood
Kungiyar MOPPAN na shirin hana fim din soyayya a masana’antar Kannywood
Asali: Twitter

"Idan kuma muka ga na soyayya ne, to za mu dakatar da shi kuma za mu ci gaba da daukar wannan mataki har tsawon wani lokaci."

KU KARANA KUMA: Zamfara: An ba hammata iska tsakanin magoya bayan APC da PDP a harabar kotun koli

Ya ce bayan sun gamsu da yadda aka tabo wasu sassan rayuwa, za su ci gaba da yin fina-finan soyayyar.

Sai dai wasu masu shirya fina-finai sun fara tofa albarkin bakinsu kan wannan batu.

Ali Ali wani mai koyar da rawa ne a fina-finan Hausa ya ce hana su yin fina-finan soyayya kamar kashe harkar fina-finan Hausa ne.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng