Kotu ta bada oda a kamo tsohon gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu

Kotu ta bada oda a kamo tsohon gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu

-Wata babbar kotun tarayya dake garin Minna ta bayar da umarnin kamo tsohon gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu tare da tsohon dan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar PDP Umar Nasko

- Kotun ta bada umarnin ne bayan ta nemi su bayyana a gabanta domin cigaba da sauraron kararsu amma suka yi watsi da gayyatar kotun

Jiya Alhamis 23 ga watan Mayu, 2019, alkalin babbar kotun tarayya dake garin Minna babban birnin jihar Neja, Mai Shari'a A.B. Aliyu, ya soke belin da ya bai wa tsohon gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu da kuma tsohon dan takarar gwamnan jihar na jam'iyyarPDP, Alhaji Umar Gado Nasko.

Alkalin, wanda ya nuna bacin ranshi sosai da tsohon gwamnan Aliyu da Nasko suka ki bayyana kansu a kotu, duk da cewar an sanar da su za a cigaba da sauraron shari'arsu, alkalin ya sanya a kamo su saboda kin bin dokar kotu da suka yi.

Kotu ta bada oda a kamo tsohon gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu
Kotu ta bada oda a kamo tsohon gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu
Asali: Facebook

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa na tuhumar Babangida Aliyu da Umar Nasko, akan zargin hannu a badakalar fitar da kudi kusan naira biliyan biyu ta hanyar da ba ta dace ba, da kuma wasu laifuka na daban. An gurfanar da wadanda ake zargin a gaban mai shari'a Bogoro Yelin, inda kuma suka amsa laifinsu akan laifin da ake tuhumar su dashi.

Sai dai kuma an sauyawa alkalin kotu, inda a yanzu ya koma sauraron shari'ar zabe da aka shigar. Daga baya an danka shari'ar ga mai shari'a A.B. Aliyu, wanda a yanzu shine yake sauraron karar.

KU KARANTA: Kano: Ma'aikata sun shiga dar-dar yayin da Ganduje ya ciyo bashin dala miliyan 95

A yau da ya kamata mu cigaba da sauraron kararsu, babu wanda ya bayyana daga su har lauyoyinsu. Lauyan daya daga cikin masu laifin Mista Osuman Mamma (SAN) ya rubutowa kotu takardar cewar yana kotun sauraron karar zabe.

Amma da aka tambayi babban mai bada shawara ya bayyana cewa bai tura kowa domin ya wakilce shi a kotu ba. Hakanne ya tilasta kotun ta janye belin da ta bai wa masu laifin sannan ta sanya a kamo su cikin gaggawa.

A karshe dai alkalin kotun ya daga sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Mayu, 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel