Shugaba Buhari ya taya Modi murnar lashe zabe

Shugaba Buhari ya taya Modi murnar lashe zabe

Shugaba Muhammadu Buhari ya mika sakon taya murna ga zababen Farai Minista Narendra Modi na kasar India da jam'iyyar Bharatiya Janata Party (BJP) a kan nasarar da ya yi na lashe zabe.

A cikin sakon da hadimin shugaba Buhari kan kafafen yada labarai, Femi Adesina ya fitar a ranar Alhamis a Abuja, ya ce Shugaba Buhari ya ce kasar Indiya ce babban abokiyar cinnikayar Najeriya kuma ya mika godiyarsa bisa zumuncin da ke tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Buhari ya taya Modi murnar lashe zabe

Shugaba Buhari ya taya Modi murnar lashe zabe
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Manyan jaruman Kannywood uku sun samu wata babban kwangila

A cewarsa, shugaban kasar yana fatan fadada hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu a fanin makamashi, gine-gine, aikin noma, sarrafa kayayaki da kiwon lafiya.

Ya ce a karkashin mulkin Farai Minista Modi ne Indiya ta karbi bakuncin taron India da Afirka a Oktoban 2015 inda ya ambacci Najeriya a matsayin babban abokiyar cigaba da nahiyar Afirka.

Shugaban na Najeriya ya yiwa Farai Minisatan na India fatan alheri a sabon ofishinsa tare da samun nasara da cigaba ga jama'ar kasar demokradiyya mafi girma a duniya kamar yadda kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel