Gwamnatin tarayya, jahohi da kananan hukumomi sun kasafta naira biliyan 617

Gwamnatin tarayya, jahohi da kananan hukumomi sun kasafta naira biliyan 617

Rabe raben gwamnatocin Najeriya guda uku da suka hada da gwamnatin tarayya, gwamnatin jahohi 36 da kuma gwamnatin kananan hukumomin 774 sun rabashe yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasafta musu jimillar kudi naira biiyan dari shida da goma sha bakai da miliyan hamsin da bakwai (N617,057,000,000).

Majiyar Legit.ng ta ruwaito hukumar kididdiga ta kasa ce ta sanar da wannan alkalumma cikin wani rahoto data fitar a ranar Laraba, 22 ga watan Mayu, inda tace an samu wadannan kudade ne a watan Maris, kuma aka rabma ma gwamnatocin a watan Afrilu.

KU KARANTA: Kashe kashe: Akalla Sakkwatawa da Zamfarawa 20,000 sun yi gudun hijira zuwa Nijar

Rahoton tace naira biliyan 446,65 ya fito ne daga asusun bai daya, naira biliyan 92.18 daga asusun harajin da ake daurawa a cinikayya na VAT, naira biliyan 10 daga asusun NNPC, biliyan 13.09 daga asusun canjin kudin kasashen waje sai kuma naira biliyan 55 daya fito daga asusun harajin kaya.

Haka zalika rahoton ya fayyace gwamnatin tarayya ta samu naira biliyan 257.76, jahohi 36 sun samu biliuan 168.25 yayin da kananan hukumomi suka samu biliyan 126.58, babban birnin tarayya Abuja ta samu naira biliyan 5.49, sai kuma naira biliyan 49.82 aka raba ma jahohi masu arzikin man fetir a matsayin hakkinsu na kashi 13.

Bugu da kari gwamnati ta baiwa hukumar tattara haraji ta kasa FIRS, naira biliyan 6.15, hukumar yaki da fasa kauri ta kwastam naira biliyan 5.12 da kuma hukumar kula da arzikin man fetir ta DPR naira biliyan 3.87 a matsayin kudin gudanar da ayyukan karbar haraji.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel