An sako shugaban mafarauta da aka sace bayan an biya N1.5m

An sako shugaban mafarauta da aka sace bayan an biya N1.5m

An sako shugaban mafarautan garin Ibokun da ke karamar hukumar Ibokun a jihar Osun da aka sace a ranar Litinin tare da wata mace mai suna Mrs Tayo George bayan biya masu garkuwa da mutanen zunzurutun kudi Naira miliyan 1.5.

Wata majiya daga garin Ibokun ta tabbatar da cewa sarkin mafarauta, Cif Amusa Dunsin (TirmiOde) da Mrs George sun koma gida wurin iyalensu.

Majiyar ta ce an tsare mutane biyun ne a wata daji da ke Esa-Oke.

An sako shugaban mafarauta da aka sace bayan an biya N1.5m
An sako shugaban mafarauta da aka sace bayan an biya N1.5m
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An roki Buhari ya ajiye Lai Mohammed a karo na biyu

Ya ce, "An sako mutane biyun a daren ranar Laraba 22 ga watan Mayu bayan an biya kudin fansar da jama'ar garuruwan Ibokun, Otan-ille, Ilare, Esa-Odo, Imesi-Ile da Esa-Oke su kayi karo-karo."

"An sake su a dajin Esa-Oke inda aka ajiye wasu mutane da akayi garkuwa da su a watanni baya," a cewar majiyar.

An sace shugaban mafarautan ne da Mrs Goerge a ranar Litinin a karamar hukumar Obokun na jihar Osun yayin da suka baro Esa Odo kan hanyarsu ta zuwa Ilare a karamar hukumar Obokun.

A yayin da masu garkuwa da mutanen su kayi nasarar awon gaba da Dunsin da Mrs George, sauran fasinjoji uku daga cikin motar sun tsere.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel