Kashe kashe: Akalla Sakkwatawa da Zamfarawa 20,000 sun yi gudun hijira zuwa Nijar

Kashe kashe: Akalla Sakkwatawa da Zamfarawa 20,000 sun yi gudun hijira zuwa Nijar

Sama da jama’an jahar Sakkwato dana Zamfara mutum dubu ashirin ne suka tsere daga garuruwansu zuwa kasar Nijar don neman mafaka tare da samun saukin hare haren da yan bindiga suke kai musu babu gaira babu dalili suna kashesu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnan jahar Maradi ta kasar Nijar, Zikiri Umar ne ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da yake a gidan talabijin na kasar Nijar, inda yace yan gudun hijiran sun shiga Nijar ne sakamakon matsalar tsaro data dabaibaye yankin Sakkwato da Zamfara.

KU KARANTA: Gwamna El-Rufai zai baiwa yara marasa galihu dubu 145 ilimin boko kyauta a Kaduna

Haka zalika rahoton gidan talabin ya bayyana cewa akalla yan gudun hijiran sun kwashe sama da watanni goma a sansanin da suke fakewa, shima hakimin Madarufa da Gidan Rinji na kasar Nijar, Saleh Jibo ya shawarci jama’an kauyen dasu taimaka ma yan gudun hijiran, a cewarsa Nijar da Najeriya duk daya ne.

“Matsalar tayi kamari a wannan karo, mutane basu da amincin tsaro a gidajensu, ya zama dole su yi gudun hijira zuwa kasashen dake makwabtaka dasu don samun sauki.” Inji Jaafaru Bagwari, shugaban yankin Barikin Suburi.

Ko a kwanakin baya, a ranar 10 ga watan Mayu, sai da gwamnan jahar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya tabbatar da tserewar wasu jama’an jahar Sakkwato zuwa Nijar don neman mafaka daga hare haren yan bindiga.

Sai dai gwamnan ya dauki alwashin dawo dasu gida Najeriya, tare da tabbacin basu tsaron lafiyarsu data dukiyarsu, inda yace “Ina kira ga jama’an Burunkuma da kewaye dasu daina gudun hijira zuwa Nijar, zan tafi da kaina zuwa sansaninsu a Nijar din domin na roki sauran dasu dawo Najeriya.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel