Dalilai 5 da ke hana mata aure a yankin arewa

Dalilai 5 da ke hana mata aure a yankin arewa

Kamar yadda muka sani aure sunnah ce ta Annabi Muhammadu (SAW) kuma burin iyaye shine ace yau an wayi gari suga ‘yarsu a dakin mijinta idan hart a kai munzalin aure, musamman a yanki na Arewacin Najeriya.

A lokutan baya mace kan zama abin nunawa a idon duniya, idan har ta kai wani shekaru bata yi aure ba. Abin ma har ya kan shafi zaurawa mata da matan da suka ki aure bayan mazajen su suka rasu.

Sai dai a zamanin nan da muke ciki abun ya sha bamban, domin sai ka ga mace ta girma har wuci aure amma tana gaban iyayenta saboda wasu dalilai wanda mafi akasarinsu ba kwarara bane.

Dalilai 5 da ke hana mata aure a yankin arewa

Dalilai 5 da ke hana mata aure a yankin arewa
Source: UGC

Ga wasu daga cikin dalilan da ake ganin suna hana matan arewa aure a wannan zamanin:

1. Kwadayi da son abin duniya: A wannan zamani da muke ciki, mata da dama sun daukar wa kansu dala ba ganmo, inda son jin dadi da watayawa kan sa zaman aure ya gagare wasu da yawa. Wasu matan kan so a yi ta jin dadi ne. Idan miji ya samu kararyar arziki shike nan sai ta yi ta dabalbale sa da fitina. Nayau dabam da na gobe. duk don ta samu damar sheke ayar ta a waje ta yi abin da taga dama.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun hallaka yan sa kai 5 a jihar Katsina

2. Daidaita jinsin Mace da Namiji: Yanzu akwai kungiyoyi da suka fito suna kira ga mata da su nemi hakkin su a wajen mazajen su. Cewa daidai suke da maza. Idan Ta goya yaro shima gobe ya goya yaron Sannan ma su raba ranakun girki da wanke- wanke. Duka irin haka na dada rudin mata wajenkin zaman aure.

3. Yaudara: Wasu matan kan fada tarkon mazaje masu yaudara. Idan har mace bata yi sa’an samun nagari ba sai kaga ta fada cikin irin wannan hali da hakan sai ya sa ayi ta fama da ita. Taki yi auren ko kuma ma sauraren wani namiji.

4. Nuna Isa: Kamar yadda suka bayyana. Mata a wannan zamani suna son ace suma sai yadda suke so za ayi. Hakan yasa wasu da dama basu iya zama karkashin wani namiji da sunan wai a karkashin shi suke. Idan tana zamn kanta to zata yi abinda da take so babu mai takura mata.

5. Tsananin talauci da Dogon Buri: Wannan shima babban matsala ce da ake fana da shi a wannan zamani da muke ciki. Rashin abin hannu da kuma cika tumbi da aka yi da burin tsiya kan sa mata su ki yin auren kwata-kwata ko kuma ma da sun yi su ki zama.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel