Wike ya yi alkawarin bani cin hancin biliyoyin naira idan na taya shi magudin zabe - Janar Jamil Sarham

Wike ya yi alkawarin bani cin hancin biliyoyin naira idan na taya shi magudin zabe - Janar Jamil Sarham

A kokarin da yake na ganin ya kare kanshi daga zargin da gwamnan jihar Rivers yake yi masa na cewa ya tura a kasheshi, sannan kuma yana da hannu a badakalar man fetur na jihar, Janar Jamil Sarham ya bayyana cewa zargin gwamnan ya biyo bayan cin hancin da ya so ya bashi yaki karba a lokacin zabe, domin ya taya shi yin magudi

Janar Jamil Sarham, ya bayyana cewa gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya yi alkawarin bashi cin hancin biliyoyin nairori domin ayi magudin zaben gwamna a jihar.

Aminu Iliyasu, mai magana da yawun Sarham, ya ce gwamna Wike ya yanke shawarar ganin bayanshi, bayan yaki karbar tayin cin hancin nashi.

Gwamna Wike yana zargin Sarham da badakalar man fetur a jihar, da kokarin kasheshi a ranar 15 ga watan Fabrairu, 2019.

Wike ya yi alkawarin bani cin hancin biliyoyin naira idan na taya shi magudin zabe - Janar Jamil Sarham
Wike ya yi alkawarin bani cin hancin biliyoyin naira idan na taya shi magudin zabe - Janar Jamil Sarham
Asali: Facebook

A lokacin da yake karyata zargin da gwamnan ya ke yi masa, yace: "Zargin da Wike yake yi mini yana da nasaba da kwarewata da kuma kin karbar tayin cin hancin biliyoyin kudi da yayi mini domin na taimaka mishi wurin yin magudin zaben gwamna a zaben da ya gabata."

KU KARANTA: 'Yan sanda sun kama mutumin da ya yiwa abokanan sa ihun kidinafas a Kaduna

"Kin karbar tayin sa ne yasa ya sanya karan tsana a kaina, kuma yake kokarin ganin bayana ta kowanne hali."

A karshe dai hukumar soji ta bukaci gwamna Nyesom Wike da ya gabatar da shaidu na zargin da yake yiwa Janar Jamil Sarham.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel