'Yan bindiga sun kashe mutane fiye da 26 a kananan hukumomi 3 dake jihar Katsina

'Yan bindiga sun kashe mutane fiye da 26 a kananan hukumomi 3 dake jihar Katsina

Wasu 'yan bindiga sun kashe fiye da mutane 26 a wani hari da suka kai a kan mazauna wasu garuruwa dake kananan hukumomin Dan Musa, Faskari da Batsari dake jihar Katsina.

Majiyar mu ta sanar da mu cewar 'yan bindigar sun kai harin ne ranar Talata a kan babura.

A cewar majiyar, an kashe mutane 11 a garin Sabon Layin Galadima dake karkashin karamar hukumar Faskari, yayin da aka kashe mutane biyar a Mara Zamfarawa dake karamar hukumar Dan Musa tare da sace dabbobi da dama.

Gidan Talabijin na Channel ya rawaito cewar 'yan bindigar sun kai wa wasu manoma hari a gonakin su a kauyen 'Yar Gamji dake karamar hukumar Batsari, inda suka kashe mutane 18, yayin da aka rasa mutane 10.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce wadanda aka kashe a karamar hukumar Faskari mambobin kungiyar bijilanti ne.

'Yan bindiga sun kashe mutane fiye da 26 a kananan hukumomi 3 dake jihar Katsina

Gwamnan jihar Katsina; Aminu Bello Masari
Source: UGC

A cewar sa, "wasu 'Yansakai a kauyen Sabon Layi a karamar hukumar Faskari sun bi 'yan bindigar cikin daji tun jiya amma har yanzu basu dawo ba. Mazauna kauyen sun samu nasarar gano gawar mutum biyu daga cikin su kuma tuni sun binne su.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun tsare wata shu'umar ungulu bayan jama'a sun kai rahoton ta a Aadamwa

"Mun tura runduna 'yan sanda karkashin jagorancin DPO din Faskari domin nemo ragowar kuma su ma sun yi nasarar gano karin gawar mutane uku. Kazalika mun gano wani sansani da 'yan ta'addar suka taba amfani da shi. Muna cigaba da gudanar da bincike," a cewar DSP Isah.

A dangane da harin Dan Musa da Batsari, DSP Isah ya ce rundunar 'yan sanda tana kokarin samun karin bayanai.

"Muna kokarin samun rahotanni har yanzu," a cewar sa.

Ya kara da cewa "ya kamata jama'ar gari su fahimci irin kokarin da muke yi tare da hada kai da mu ba wai suke kushe mu, suna sukar musu ba. Rayuwar mu muke sadaukar wa domin kare jama'a. Kamata yai a yaba mana a kan hakan ba wai ake zagi da sukar mu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel