Shugaban kasar Faransa ya gayyaci Buhari zuwa wani muhimmin taro

Shugaban kasar Faransa ya gayyaci Buhari zuwa wani muhimmin taro

Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya gayyaci shugaban kasa Muhammdu Buhari zuwa wani taron kasashen Afrika da za a yi a garin Bordeaux a watan Yuni.

Sakatariyar taron kasashen Afrika da za a yi a kasar Farance, Stephanie Rivoal, ce ta sanar da hakan yayin da ta ziyarci ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, ranar Talata a Abuja.

Ta ce babban makasudin shirya taron mai taken "gina birane" shine taimakon kasashen Afrika wajen magance matsalar nan da ta addabi kasashen Afrika ta yawan hijirar da jama'ar kauyuka ke yi zuwa birane.

A cewar ta, ana sa ran Najeriya za ta gabatar da aiyukan da tayi na gina birane ga masu ruwa da tsaki da zasu halarci taron.

Ta ce shugaba Macron na da burin ganin shugaban kasar Najeriya ya halarci taron saboda muhimmancin da Najeriya keda shi a nahiyar Afrika.

Shugaban kasar Faransa ya gayyaci Buhari zuwa wani muhimmin taro

Macron da Buhari
Source: Depositphotos

Ta kara da cewa taron zai sha banban da ragowar tarukan da saba gudanar wa, saboda za a samar da hanyoyin warware kalubalen da birane a nahiyar Afrika ke fuskanta.

"Za mu ji dadin ganin shugaba Buhari da tawagar sa a wurin taron da zai taimaka wa kasashen Afrika su gina birane da raya wadanda suke da su.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun tsare wata shu'umar ungulu bayan jama'a sun kai rahoton ta a Aadamwa

"Ministocin kasashe zasu tattauna tare da musayar ilimi da hanyoyin warware raya karkara da birane.

"Ma su ruwa da tsaki zasu halarci taron domin duba abubuwan da suka fi dacewa da kuma wadanda jama'a ke bukata a birane

"Bayan haka, masu ruwa da tsaki zasu taimaka wajen bayar da shawarwari da kuma shiga a dama wasu wajen warware kalubalen da birane ke fuskanta a nahiyar Afrika bayan kammala taron," a cewar Rivoal.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel