Yan Shia sun harba nukiliya kasar Makkah yayin da Musulmai ke gudanar da Umarah
Hukumar sojan sama ta kasar Saudiyya ta bayyana cewa ta dakile yunkurin wasu munanan hare hare da kungiyar mayakan yan Shia ta Houthi dake kasar Yemen ta kaddamar ta hanyar jefa makamai masu Linzami kasar Saudiyya.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan shian sun harba makaman ne da nufin su isa biranen Makkah da Jiddah, amma Allah bai basu nasara ba sakamakon rundunar Sojan saman Saudiyya ta tarwatsa makaman tun basu kai ko ina ba a sama.
KU KARANTA: Wadanda suka yi garkuwa da surukar gwamnan jahar Katsina sun shiga hannu
Idan za’a tuna a yanzu haka dubun dubatan Musulmai ne suke gudanar da aikin Umarah a birnin Makkah, daga cikinsu akwai Maza, Mata da kananan yara daga dukkanin sassan duniya, inda ko a jiya sai da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya shirya taron shan ruwa da Tinubu a Makkan.
Sai dai gwamnatin kasar Yemen wanda ke kawance da kasar Saudiyya ta bayyan rashin dadinta game da wannan hari tare da yin tofi Allah tsine da wannan hari da ta bayyanashi a matsayin ta’addanci.
Abin mamakin shine wannan hari na makamai masu linzami da kungiyar yan shia ta Houthi ta aika kasar Saudiyya yazo ne a daidai lokacin da aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da Sojojin Yemen dake samun goyon bayan Saudiyya a yakin basasan da suka kwashe shekara da shekaru suna fafatawa.
Rahotanni sun bayyana cewa a iya shekaru hudu da aka kwashe ana gwabza wannan yaki an kashe sama da fararen hula dubu shida da dari takwas (6,800), an jikkata mutane dubu goma da dari bakwai (10,700) tare da jefa dubun dubata cikin halin gudun hijira.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng