Buhari ya sha ruwa da Tinubu, Sultan, Sarkin Kazaure da wasu manya a Saudiyya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha ruwa tare da jagoran jam'iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, da mai alfarma sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar III, da ragowar wasu manya 'yan Najeriya a kasar Saudiyya.
Buhari ya ziyarci kasar Saudiyya ne domin gabatar da aikin Umrah.
Ganawar ta shugaba Buhari da Tinubu da ragowar manyan mutanen na zuwa ne a daidai lokacin da ya rage kwanaki kalilan a rantsar da shi a matsayin zababben shugaban kasar Najeriya a karo na biyu.
A cewar jawabin da kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar, Tinubu ya yi amfani da damar shan ruwa tare da Buhari da ragowar manyan mutanen wajen yin kira ga shugabanni da jagorori a Najeriya su guji yin furucin da kan iya haddasa fitina.
A wurin taron shan ruwan akwai sarkin Kazaure, Najib Hussaini Adamu, da ragowar wasu hadiman shugaba Buhari da wakilan gwamnati dake cikin tawagar shugaban kasa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng