Kungiyoyi 22 a Kano sun bawa sabbin sarakunan jihar umarnin gaggauta sauka daga mukaman su

Kungiyoyi 22 a Kano sun bawa sabbin sarakunan jihar umarnin gaggauta sauka daga mukaman su

Gamayyar wasu kungiyoyi 22 a jihar Kano sun yi kira ga sabbin sarakunan da aka nada a jihar da su gaggauta yin murabus ba tare da wani bata lokaci ba.

A ranar 8 ga watan Mayu ne, gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kirkira sabbin masarautu hudu dake da sarakunan yanka masu daraja daya da ta sarkin Kano, jama'a na ganin shawarar gwamnan tamkar bita da kulli ne ga sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

A wani taro da manema labarai da gamayyar kungiyoyin suka yi a karkashi inuwar 'Renaissance Coalition', sun yi kira ga mai alfarma sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar III, da ya ki amince wa da sabbin sarakunan.

Sun ce sun yi wannan kira ga Sultan din ne saboda kasancewar sa babban sarki a karkashin daular Danfodiyo, wacce keda ikon warware nadin sabbin sarakunan da gwamnatin jihar Kano tayi.

Kungiyoyin sun ce gwamna Ganduje ya dauki shawarar kirkirar sabbin masarautun ne ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki ko bin ka'ida ba.

Kungiyoyi 22 a Kano sun bawa sabbin sarakunan jihar umarnin gaggauta sauka daga mukaman su

Ganduje yayin bikin nadin sabbin sarakuna a jihar Kano
Source: Twitter

Kazalika, sun yi wani kiran ga dattijan jihar Kano da su nesanta kan su, a boye ko a bayyane, daga sabbin masarautun da sarakunan da aka nada

"Muna masu Alla-wadai da halayyar gwamnatin Ganduje bisa rashin girmama dattijan mu musamman yukurin wulakanta masarautar Kano ta hanyar kirkirar sabbin masarautu," a cewar kungiyoyin.

DUBA WANNAN: Kudin LGAs: Gwamnoni sun bukaci ya tsawatar wa NFIU a kan sa musu ido

Kungiyoyin sun bayyana cewar jihar Kano na fuskantar dumbin matsaloli amma maimakon gwamnatin Ganduje ta mayar da hankali wajen ganin ta warware matsalolin da suka mamaye jihar, ta buge da fada da masarauta saboda dalilan siyasa.

"Jihar Kano ce kan gaba wajen yawan yaran da basa zuwa makaranta saboda rashin samun tallafi da goyon bayan gwamnati. Sannan ita ce kan gaba wajen yawan cunkuson yara a aji, ana samun dalibai 150 zuwa 200 a aji guda.

"Akwai kimanin fiye da mutum miliyan biyar da basa samun ruwan sha mai tsafta a jihar Kano. Jihar Kano na cikin jihohin da ake yawan samun matsalar mutuwar jarirai. Kano ce kan gaba a yawan masu sha da tu'ammali da miyagun kwayoyi," a cewar kungiyoyin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel