Mayakan Boko Haram sun kai hari Askira-Uba, sun yi awon gaba da kayan abinci mai yawa

Mayakan Boko Haram sun kai hari Askira-Uba, sun yi awon gaba da kayan abinci mai yawa

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai garin Lassa dake karkashin karamar hukumar Askira-Uba a jihar Borno tare da kone gidaje da shaguna da kuma yin awon gaba da kayan abinci mai yawan gaske da sauran kayan amfani.

Wata majiya mai tushe, da harin ya shafi 'yan uwan ta, ta shaida wa jaridar Daily Trust a Maiduguri cewar mayakan sun kai hari garin ne da misalin karfe 8:10 na daren ranar Asabar, inda suka yi harbin iska kafin daga bisani su fara kone gidaje da shagunan mutane.

Garin Lassa ya yi suna wajen harkar noma da kasuwancin kayan abinci.

Majiyar ta bayyana cewar mayakar sun fi karfin dakarun sojin dake garin na Lassa a yayin da suka so dakatar da su, amma daga baya bayan karin dakarun soji sun zo daga Askira-Uba, sojojin sun kori mayakan kafin karfe 12:00 na dare.

Mayakan Boko Haram sun kai hari Askira-Uba, sun yi awon gaba da kayan abinci mai yawa
Mayakan Boko Haram
Asali: UGC

Kazalika ta bayyana cewar ba ta da masaniyar ko an samu asarar rai sakamakon kai harin, tare da fadin cewar mayakan sun kai harin ne domin su kwashi kayan abinci da ragowar kayan amfani.

"Tabbas an yi musayar wuta tsakanin dakarun soji da mayakan kungiyar Boko Haram amma babu rahoton samun asarar rai.

DUBA WANNAN: An kama 'yan Boko Haram 4 da suka gudu zuwa jihar Edo

"Mazauna garin sun gudu zuwa cikin jeji da kuma makwabtan kauyuka dake kewaye da garin Lassa," a cewar majiyar.

Hukumomin tsaro basu fitar da sanarwa ga manema labarai ba a kan harin da kuma wasu hare-haren da kungiyar ta Boko Haram ta kai wasu kauyukan jihar Borno a kwanakin baya bayan nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel