Yadda wani jarumin kare ya ceto rayuwar wani jariri da aka binne da rai

Yadda wani jarumin kare ya ceto rayuwar wani jariri da aka binne da rai

Wani kare a yankin arewacin kasar Thailand ya ceto rayuwar wani jariri wanda ba a dade da haihuwa ba, daga cikin wani rami da aka haka aka binneshi a ciki da ranshi

Ana zargin cewa mahaifiyar jaririn ce wacce ake tunanin ta ke da shekaru 15 a duniya ta binne shi a ramin.

An gano cewa mahaifyar jaririn ta yi hakan ne saboda gudun magana da tsoron iyayenta, wadanda ba su da masaniya akan juna biyun ta ballanta kuma suga cewa ta haihu.

Mutumin da ya ke da karen, ya bayyana cewa karen nasa wanda ya sanyawa suna Ping Pong, ya binciko jaririn ne a daidai lokacin da ya ke tona wani rami a wani fili, yana cikin tona ramin ne sai ya hango kafar jaririn.

Yadda wani jarumin kare ya ceto rayuwar wani jariri da aka binne da rai
Yadda wani jarumin kare ya ceto rayuwar wani jariri da aka binne da rai
Asali: Facebook

Yana ganin kafar jaririn sai ya fara haushi, har dai mai karen ya gane cewa lallai akwai wani abu da karen ya gani, cikin gaggawa ya garzaya gurin karen, yana zuwa sai yaga ashe jariri ne karen har ya fara kokarin janyo shi daga ramin domin ya gani.

Cikin gaggawa mai karen ya tono yaron daga cikin ramin, inda ya yi gaggawar garzayawa da shi zuwa ofishin 'yan sanda mafi kusa dasu.

KU KARANTA: Hanyoyin da Dangote ya bi ya hana Ganduje tsige Sarkin Kano

Ba tare da bata lokaci ba jami'an 'yan sandan suka garzaya da jaririn zuwa asibiti, inda aka duba lafiyarsa kuma aka yi masa wanka, a karshe dai likitocin asibitin sun bayyana cewa jaririn ya na cikin koshin lafiya.

Jami'an 'yan sandan sun gudanar da bincike sosai, inda suka gano mahaifiyar jaririn, yanzu haka dai an kai mata jaririn nata kuma an danka ta a hannun iyayenta.

A halin yanzu dai jaririn na samun kulawar mahaifiyarsa matuka inda ita kanta ta zo tana nadamar abinda ta aikata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng