Kundin Kannywood: Saura kadan ya rage na auri Nafisa Abdullahi da Fati Washa

Kundin Kannywood: Saura kadan ya rage na auri Nafisa Abdullahi da Fati Washa

Bayan wata hira da manema labarai suka yi da fitaccen jarumin fina-finan Hausan nan wato Adam Zango, ya bayyana cewa saura kiris ya rage da ya auri Nafisah Abdullahi da Fati Washa amma Allah bai yi ba

A wata hira da ya yi da manema labarai fitaccen jarumin fina-finan Hausan nan Adamu Zango ya bayyana cewa saura kiris ya rage da ya auri Nafisa Abdullahi da Fati Washa, kafin daga baya abubuwa suka sauya.

Jarumin ya bayyana hakan a wata hira da ya yi ta musamman da manema labarai akan abubuwa daban-daban da suka shafi rayuwarsa.

Kundin Kannywood: Saura kadan ya rage na auri Nafisa Abdullahi da Fati Washa
Kundin Kannywood: Saura kadan ya rage na auri Nafisa Abdullahi da Fati Washa
Asali: Facebook

Ga yadda hirar ta su ta kasance:

Mece ce dangantakar ka da Nafisa Abdullahi da kuma Fati Washa?

Na yi soyayya da Nafisa Abdullahi shekaru uku da suka gabata, kuma mu ka zo muka samu matsala irin ta soyayya wadda ba a kanmu aka fara ba. A unguwa ma, a ko ina ma ana yi. Kana son budurwarka ta na sonka, kuna soyayya sai wata matsala ta zo ta faru, ka koma ka fara neman wata kuma ka aureta.

Hakan ya faru tsakani na da Nafisa Abdullahi, kuma hakan bai hana mu cigaba da harkar fina-finanmu da kuma girmama juna ba. Babu cin mutunci babu komai.

KU KARANTA: Tsugune bata kare ba: Gwamnatin jihar Kano za ta canjawa sarkin Kano masarauta

Hakazalika, na yi soyayya da Fati Washa wacce muka kusa aure tsakani na da ita. Amma da yake rayuwa kowa na kokarin ya ga cewa ya auri wanda za su zauna lafiya, ko kuma ya auri wacce yake ganin cewa za su dace ko kuma wace irin wacce abubuwan su ya zo daya tsakaninsu, ko kuma da danginmu ko na ta za su iya cewa sun yarda da kaza ko ba su yarda da kaza ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng