Hotunan Shugaba Buhari a masallacin harami da ke Makkah yayin aikin Umrah

Hotunan Shugaba Buhari a masallacin harami da ke Makkah yayin aikin Umrah

A ranar Alhamis 16 ga watan Mayun 2019 ne Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari da tawagarsa suka isa birnin Madina na kasar Saudiyya domin gudanar da ibadar Umrah a cikin watan Ramadan mai cike da albarka.

Shugaban kasar ya samu kyakyawan tarba daga Yarima Saud Bin Khalid Al-Faifal a matsayinsa na babban bakon Sarki Salmanu inda ya fara kai ziyara masallacin Annabi da ke birnin Madinah.

Daga bisani kuma shugaban kasan ya karasa birnin Makkah inda ya ziyarci masallacin Makkah domin cigaba da ibadar na Umrah.

Fadar Shugaban kasa ta bayyana ce Buhari ya ziyarci Saudiyya ne sakamakon amsa gayyata na masarautar karkashin jagorancin Sarki Salman Bin Abdulaziz.

Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar ta bakin kakakin shugaba Buhari, Mallam Garba Shehu ya ce ana sa ran jagoran kasar zai dawo Najeriya a ranar Talata, 21 ga watan Mayun 2019.

Hotunan Shugaba Buhari da Aisha yayin gudanar da aikin Umrah
Shugaba Buhari a masallacin Makkah yayin gudanar da aikin Umrah
Asali: Twitter

Hotunan Shugaba Buhari da Aisha yayin gudanar da aikin Umrah
Hotunan shugaba Muhammadu Buhari a masallacin Makkah yayin gudanar da aikin Umrah
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Na hannun daman Atiku ya bukaci a bayyana sunayen masu shirin juyin mulki

Hotunan Shugaba Buhari da Aisha yayin gudanar da aikin Umrah
Shugaba Buhari da uwargidansa, Aisha a masallacin Makkah yayin aikin Umrah
Asali: Twitter

Hotunan Shugaba Buhari da Aisha yayin gudanar da aikin Umrah
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da sauran al'ummar musulmi yayin aikin Umrah a Makkah
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel