Ma'aikatan Zamfara sun koka kan rashin samun albashi na shekaru 5

Ma'aikatan Zamfara sun koka kan rashin samun albashi na shekaru 5

Ma'aikata 1,400 da gwamnatin jihar Zamfara ta dauka aiki a shekarar 2014 sun bukaci a biya su albashinsu na tsawon watanni 60 da sauran allawus dinsu da gwamnatin jihar ba ta biya su ba.

Ma'aikatan sunyi wannan korafin ne a karkashin kungiyar 'May 2014 Civil Servants' karkashin jagorancin shugabansu, Lukman Majidadi a yayin wata taron manema labarai da suka kira a jiya, Alhamis inda suka ce suna cikin mawuyacin hali saboda halin da gwamnatin jihar ta jefa su ciki.

Ma'aikatan Zamfara sun koka rashin biyansu albashi na watanni 60
Ma'aikatan Zamfara sun koka rashin biyansu albashi na watanni 60
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu Yanzu: Kotu ta yanke hukunci kan sauya shekan Saraki da Dogara

"Bayan jarrabawa da aka yi masa daga bisani an bawa mutane 1,351 aiki cikin 8,000 da suka nemi aikin sannan aka tura su wuraren ayyukansu tun a Mayun 2014 amma tun daga wannan lokacin ba a taba basu ko kobo ba a matsayin albashi," inji Majidadi.

A yayin da ya ke tsokaci kan lamarin, shugaban ma'aikatan jihar, Muhammadu Mujtaba Isah ya ce ba a sanya sunayensu cikin takardan biyan albashi bane saboda rashin jituwa da ke tsakanin ma'aikatan kudi da kwamitin da ta tantance sabbin ma'aikatan karkashin shugaban cibiyar ma'aikata, Ahmad Zabarma.

"Duk da cewa ba ni ne shugaban ma'aikata ba a lokacin da aka dauke su aiki, mun sake daukan sabbin ma'aikata a 2018 kuma na fada musu cewa suna iya zuwa domin a sake daukan su aiki kai tsaye kuma sun zo.

"Saboda haka maganar ma'aikata 1,400 batu ne da an gama zancen sa tuntuni. An rufe maganar," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel