Goodluck Jonathan ya yi mana alkawarin N100bn a 2015 - Miyetti Allah
Sakataren kungiyar Miyetti Allah Kautal Horre na kasa, Salah Alhassan ya ce kungiyar ta nemi gwamnatin tarayyar najeriya ta biya ta zunzurutun kudi Naira biliyan 100.
Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta karayata cewa kungiyar ta bukaci a biya ta kudi domin kare karshe hare-hare a sassan kasar nan.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a wata hira da tayi da jaridar The Punch a ranar Alhamis.
Alhassan ya ce tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ya yi alkawarin biyan su kudin kuma hakan yasa kungiyar ta cimma matsayar goyon bayan tazarcen sa a shekarar 2015.
DUBA WANNAN: Rundunar soji ta fitar da jawabi a kan zargin yunkurin kifar da gwamnatin Buhari
Da aka tambaye shi ko kudin da gwamnatin tarayyar za ta biya su na tsohiyar baki ne, Alhassan ya ce: "Wannan sharri ne kawai. Dama suna biyan irin wannan kudin ne? Sun taba biyan mu irin wannan kudin ne? Wannan Naira biliyan 100 kudin gina kananan wuraren kiwo ne da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi niyyar biya domin magance matsalar manoma da makiyaya.
"Ina tsamanin gwamnonin jihohin da ke cikin kwamitin da tsohon gwamnan Benue, Gabriel Suswan ke jagoranci sunyi amfani da wani kaso cikin kudin. Amma bana tsamanin dukkan kudin ya isa hannun makiyaya.
"Gwamnatin tarayya tana kokarin ganin yadda za ta tallafawa makiyaya su magance matsalar da ke tsakanin su da manoma ne.
"Mutanen da ke cewa an bawa Miyetti Allah N100bn domin su dena sace mutane makaryata ne kawai masu neman tayar da fitina, mun lura akwai wasu mutane da ke kokarin canja labarin."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana
Asali: Legit.ng