Mummunan hatsarin jirgin sama ya faru a kasar Dubai, mutane 4 sun sheka barzahu

Mummunan hatsarin jirgin sama ya faru a kasar Dubai, mutane 4 sun sheka barzahu

Rahotanni sun tabbatar da mutuwar yan kasar Birtaniya guda 3, da wani dan kasar Afirka ta kudu a sanadiyyar mummunan hadarin jirgin sama daya auku a ranar Alhamis, 16 ga watan Mayu a birnin Dubai dake hadaddiyar daular larabawaa, UAE.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya auku ne a gab da filin sauka da tashin jiragen sama na Dubai, a lokacin da jirgin dake dauke da mutane hudu yake kan hanyarsa ta zuwa filin domin gudanar da gyare gyare a wata na’urar filin sauka da tashin jiragen sama na Dubai.

KU KARANTA: Yadda yan Boko Haram suka tashi wasu garuruwan Adamawa cikin dare

Mummunan hatsarin jirgin sama ya faru a kasar Dubai, mutane 4 sun sheka barzahu

Mummunan hatsarin jirgin sama ya faru a kasar Dubai, mutane 4 sun sheka barzahu
Source: UGC

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasar ta bayyana cewa jirgin daya gamu da hatsarin mallakin kamfanin Diamond Aircraft ne, kuma yana da rajista a kasar Birtaniya, kuma ya gamu da hatsarin ne akan hanyarsa ta zuwa filin jirgin Dubai, daga nan ya gamu da matsalar data kaishi kasa.

Da fari, rahotanni daga gidajen watsa labaru na kasar Dubai cewa suka yi matukan karamar jirgin saman guda biyu sun mutu sakamakon matsalar na’ura, amma daga bisani cikakken bincike ya tabbatar da cewa duka mutane hudun dake ciki sun rigamu gidan gaskiya.

Sai dai duk da wannan hatsari jirage basu daina tashi da sauka a filin jirgin na Dubai ba sakamakon tana daga cikin manyan filayen jirgin sama da suka fi hada hada, sai dai kawai hukumar ya sanya matakan ko-ta-kwana don gudun sake tasowar wata matsalar anan kusa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel