Sheikh Dahiru Bauchi ya caccaki Ganduje akan muzguna ma Sarkin Kano
Fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan dake gudanar da Tafsiri a babban Masallacin mabiya darikar Tijjaniyyah dake garin Kaduna, Sheikh Dahiru Bauchi ya caccaki lamirin gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje game da kirkirar sabbin masarautu a jahar.
Legit.ng ta ruwaito Shehin Malamin yana bayyana wannan mataki da gwamnan ya dauka a matsayin cin fuska da kuma muzguna ma masarautar Kano dake da martaba a idon duniya, abinda yace ko turawan mulkin mallaka basu yi gigin yi ba.
KU KARANTA: Dalilin da yasa muka dage gudanar da zaben gwamna a Kogi da Bayelsa – INEC
“Abinda ya faru a Kano ya tsoratar da mutane, har turawan mulkin mallaka suka ci kasarnan, suka mallaki kasar, har suka gama shegantakarsu tsawon shekaru 60 basu taba masarautar Kano da sunan wargazata ba.
“Wadanda suka yi sarauta da mulki a Kano anyi kusan gwamnatoci guda 9 na mulkin Soja, 7 na farar hula, amma babu wanda ya tunkari Kano da irin wannan abinda ake tunkararta da shi a yanzu, ina nanatawa Kano ba irin sauran jahohi bane.” Inji shi.
Sai dai Shehin Malamin ya bayyana jin dadinsa da hukuncin da yace wata babbar kotu ta yanke na haramta ma Ganduje kirkirar sabbin masarautun tare da nada musu Sarakai masu daraja ta daya, inda yace hakan ya faranta masa kwarai.
Idan za’a tuna a ranar 8 ga watan Mayu ne gwamnan Kano ya kirkiri sabbin masarautu guda hudu a jahar Kano tare da nada musu sabbin Sarakuna masu daraja ta daya, masarautun da sarakunan sune kamar haka; Aminu Ado-Bayero, Bichi; Tafida Ila, Rano; Ibrahim Abdulkadir, Gaya da Ibrahim Abubakar ll, Karaye.
Sai dai manyan hakiman fadar Sarkin Kano guda hudu wadanda hakkin zaben Sarki a masarautar Kano ya rataya a wuyansu sun nuna ma Ganduje yatsa game da raba masarautar Kano, inda suka garzaya gaban kotu domin kotu ta dakatar da gwamnan.
Manyan hakiman sun hada da Madakin Kano Yusuf Nabahani, Makaman Kano Sarki Ibrahim, Sarkin Dawaki maituta, Bello Abubakar da kuma Sarkin Bai, Mukhtar Adnan hakimin Dambatta.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng