An samu sabani tsakanin Naziru Sarkin Waka da Hadiza Gabon

An samu sabani tsakanin Naziru Sarkin Waka da Hadiza Gabon

Sabani na neman shiga tsakanin Naziru Sarkin Waka da Hadiza Gabon, bayan da ya yi wani shagube a shafinsa ita Hadiza Gabon kuma ta nuna rashin amincewarta akan maganar da yayi din

Wata irin zazzafar muhawara ta barke tsakanin Naziru Ahmad Sarkin Waka da fitacciyar jarumar fina-finan Hausan nan Hadiza Aliyu Gabon.

Mawakin Naziru Ahmad, wanda Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya nada mukamin Sarkin Mawakan Kano, yayi wani shagube a shafinsa kan mutane masu yin kyauta kuma suje kafafen sada zumunta suna yadawa domin duniya ta gani.

An samu sabani tsakanin Naziru Sarkin Waka da Hadiza Gabon
An samu sabani tsakanin Naziru Sarkin Waka da Hadiza Gabon
Asali: Facebook

Mawakin ya ce, "Yin hakan bai kamata ba ko kadan saboda kamar izgilanci ne da cin fuska ga wanda ka bai wa sadakar idan har ka yada shi a shafin sada zumunta."

Sai dai kuma mawakin bai jima da wallafa sakon nashi ba, sai fitacciyar jarumar fina-finan Hausan nan Hadiza Aliyu Gabon ta maida masa martani inda take bayyana cewa; "Yana da kyau, kuma ya kamata idan mutane suka yi kyauta su sanya a kafafen sada zumunta domin hakan shi ne zai taimaka wurin jawo hankalin wasu suyi koyi da masu taimakawa marasa karfin."

KU KARANTA: Wata yarinya ta kashe kanta bayan ta nemi abokanta na Instagram su taya ta zabi tsakanin mutuwa da rayuwa

Hadiza Gabon kowa yayi mata kyakkyawan sani akan taimakon gajiyayyu, marayu, da talakawa, musamman a wata irin wannan mai alfarma.

Idan ba a mance ba majiyarmu LEGIT.NG ta kawo muku rahoton sabanin da jarumar Hadiza Gabon ta samu tsakaninta da Amina Abdullahi Amal, lamarin ya kawo cece-kuce a kafar sadarwa inda mutane da yawa suke ganin cewa abinda Hadiza gabon ta yi bai kyauta, har suke bai wa Amina Amal shawarar ta kai ta kara kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel