Jihar Borno ta fi wasu jihohin Najeriya da dama kwanciyar hankali - Shettima

Jihar Borno ta fi wasu jihohin Najeriya da dama kwanciyar hankali - Shettima

A ranar Laraba da ta gabata gwamnan jihar Borno Kashim Shettima, ya bayyana cewa duk da jihar sa na ci gaba da fama da ta'addancin kungiyar masu tayar da baya ta Boko Haram tsawon fiye da shekaru goma, akwai wasu jihohin Najeriya dama ta dara su ta fuskar kwanciyar hankali.

Gwamnan jihar Borno ya ce duk da jihar sa na ci gaba da fuskantar kalubale na ta'addancin mayakan Boko Haram, akwai jihohin da ta dara ta fuskar samun kwanciyar hankali wajen gudanar da harkokin kasuwanci.

Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima
Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima
Asali: Facebook

A sakamakon annobar ta'addancin masu garkuwa da mutane da wasu miyagun ababe da suka zamto ruwan dare, gwamna Kashim ya ce jihar Borno ta kere jihohin Kaduna, Sakkwato, Zamfara, Katsina da kuma birnin Abuja ta fuskar samun nutsuwa da kwanciyar hankali na aiwatar da harkokin kasuwanci.

Furucin gwamna Kashim ya zo a yayin karbar bakuncin tawagar shugaban kwamitin 'yan majalisar wakilai akan harkokin da suka shafi dakarun sojin kasa na Najeriya, Rima Shawulu yayin da ta ziyarci fadar gwamnatin sa da ke birnin Maiduguri.

KARANTA KUMA: PDP ta nemi a sake a zaben gwamna a jihar Kwara

Cikin kalaman sa, "a halin yanzu jihar Borno ta kere garin Abuja, Zamfara, Katsina, Sakkwato da kuma Kaduna ta fuskar zaman lafiya da samun nutsuwa ta kwanciyar hankali a sakamakon rashin fitintinu da ta'addancin masu garkuwa da mutane,'yan baranda ko kuma fashi da makami".

A wani rahoton mai nasaba da wannan, gwamnatn tarayyar ta batar da kimanin Naira Biliyan biyar cikin tsawon shekaru uku wajen bayar da agajin jin kai na lafiya kamar yadda ministan lafiya ya bayar da shaida, Farfesa Isaac Adewole.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng