Hukumar DSS ta cafke manyan Malaman Musulunci guda 2 a Katsina da Bauchi

Hukumar DSS ta cafke manyan Malaman Musulunci guda 2 a Katsina da Bauchi

Rundunar hukumar tsaro ta sirri, DSS, ta yi ram da wasu manyan Malaman addinin Musulunci a jahohin Katsina da Bauchi, Sheikh Aminu Usman inkiya Abu Ammar da kuma Ustaz Idris Abdulaziz biyo bayan gayyatar da hukumar tayi musu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kimanin kwanaki biyar da suka gabata ne hukumar DSS ta gayyaci Ustza Idris zuwa ofishinta dake jahar Bauchi domin amsa wasu tambayoyi, sai dai daga nan kuma suka yi awon gaba dashi zuwa babban birnin tarayya Abuja don cigaba da yi masa tambayoyi.

KU KARANTA: Matasan Najeriya sun jinjina ma Buhari game da wani muhimmin aiki da yasa a gaba

Hukumar DSS ta cafke manyan Malaman Musulunci guda 2 a Katsina da Bauchi
Idris da Abu Ammar
Asali: UGC

Wani daaga cikin almajiran Malam ya bayyana cewa tun ranar Asabar din data gabata basu samu damar tattaunawa dashi ba balle su san halin da yake ciki. Sai dai shugaban daliban Malam na majalisin Dutsen Tanshi Majlis Foundation Malam Yau Idris yace:

“Duk wani mutum ko kungiya da ta shiga tayar da hankali ko rikici a dalilin kama Malam da DSS tayi bata tare damu, kuma bada izinin majalisinmu ko izinin Malaminmu Idris Abdulaziz Bauchi itayi hakan ba, ko wanene kuwa.” Inji shi.

Shi kuwa Malam Abu Ammar ya shiga hannu ne bayan hukumar DSS ta gayyaceshi zuwa ofishinta a ranar Talata, 14 ga watan Mayu bayan wani wa’azi da yayi yana sukar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari game da tabarbarewar tsaro a Najeriya.

Abu Ammar yana tare da wani abokinsa mai suna Malam Shamsu a lokacin da DSS suka kirashi a waya suna gayyatarsa zuwa ofishinsu dake kan hanyar Daura a garin Katsina, sai suka tafi tare da Shamsu, amma daga bisani suka nemi Shamsu ya tafi yayin da ake gab da shan ruwa.

Idan za’a tuna hukumar DSS ta taba kama Malam Abu Ammar a watan Maris shekarar 2015 biyo bayan wasu kalamai daya furta akan tsohon gwamnan jahar Katsina, Ibrahim Shehu Shema.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng