Yan bindiga sun kashe yan jaharmu 33 cikin mako guda – Matasan Katsina

Yan bindiga sun kashe yan jaharmu 33 cikin mako guda – Matasan Katsina

- Ayyukan yan bindiga a Katina na ci gaba da haifar da tsananin damuwa

- An sanar da yan sanda batun kisan yan jahar 33 da yan bindiga suka yi a cikin mako guda

- Matasan yankin Batsari da ke jihar sun bayyana cewa yankin ya fara zama garin fatalwa saboda yawan hare-hare da yan bindigan ke kaiwa

Matasa daga yankin Batsari a jihar Katsina a jiya sun ce yan bindiga sun kashe mutane 14 a hanyar Batsari-Safana a jihar a ranar Litinin.

Matasan wadanda suka samu wakilcin Gali Iliyasu Batsari, karkashin kungiyar Batsari Youth Forum, sun kuma bayyana cewa yan binddigan kashe mutane 19 duk a cikin mako guda.

Sun bukaci a sako wassu mambobin yan bangan da yan sanda suka kama bisa zargin kashe wani wanda ake ikirarin dan bindiga ne.

Matasan sunyi zanga zanga akan yawan hare haren da yan bindigan ke kai ma mutanen yankin da kauyukan kewaye.

Yan bindiga sun kashe yan jaharmu 33 cikin mako guda – Matasan Katsina
Yan bindiga sun kashe yan jaharmu 33 cikin mako guda – Matasan Katsina
Asali: UGC

Kakakin kungiyar, Gali, yace Batsari ta zamo inda mutane ke gudun hijira don tsira a kulla yaumin.

A cewar shi, rayuwa a garin ya zama abun damuwa saboda shigowan yan bindiga da miyagun mutane wadanda ke harin kauyen da kisan al’umma.

KU KARANTA KUMA: Nadin sarakuna: Kwamishinan Ganduje yayi karin haske kan umarnin Kotu

Yayin da yake bayyana ra’ayinsa, kakakin rundunar yan sandan jiar, Gambo Isah, ya tabbatar da kama jami’in bangan, inda ya bayyana cewa a kundin tsarin kasa, basu da damar daukan ran kowa.

Ya ce: “ Matakin da muka dauka shine mafi alkhairi gare mu, baza ka dauki doka a hannunka ba kamar yanda kundin tsari tayi bayani, kuma kar wanda ya kashe wani.

“Sun kashe shi kawai don suna zargin shi da hannu cikin lamarin, baza ka iya yakan laifi da laifi ba, muna binciken lamarin da ya shafi kisa da kuma hare hare dake faruwa a yankin.

“Idan muka zauna ba tare da daukan mataki ba kuma muka bar mutane suna daukan doka a hannunsu, zamu kasance tattare da rashin tsaro. Bamu son rigingimu su kaimu ga lamarin rashin tsaro.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel