Obasanjo ne mutumin da yafi kowa cin amana a Najeriya - Sarkin Legas

Obasanjo ne mutumin da yafi kowa cin amana a Najeriya - Sarkin Legas

- Sarkin Legas ya caccaki tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, inda ya ce babu babban maciyin amana kaf Najeriya irin Obasanjo

- Ya ce bai ji dadin yadda ya fito kir-kiri ya nuna adawar shi akan shugaba Buhari ba, duk kuwa da yasan cewa shine wanda zai kawo cigaba a kasar nan

Sarkin Legas, Oba Rilwan Akiolu, ya bayyana tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a matsayin mutumin da yafi kowa kawo rikici a kasar nan.

Akiolu wanda ya dauki tsawon lokaci suna musayar harshe da tsohon shugaban kasar, ya bayyana haka yayin da wasu mutane suka kai mashi ziyara fadarsa da ke birnin Legas, jiya Laraba.

Sarkin wanda ya bayyana yadda zaben 2019 ya gudana, ya bayyana yadda kiri-kiri tsohon shugaban kasar ya juyawa shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben da ya gabata, inda ya nuna goyon bayanshi ga Atiku Abubakar.

Obasanjo ne mutumin da yafi kowa cin amana a Najeriya - Sarkin Legas
Obasanjo ne mutumin da yafi kowa cin amana a Najeriya - Sarkin Legas
Asali: UGC

"Daman ba tun yanzu ba na fadi cewa Buhari ne zai lashe zabe, abin takaici sai gashi, mutumin da yafi kowa matsala a kasar nan, tsohon shugaban kasa Obasanjo. Ya mance da cewa Allah ne ya ke yin komai, inda ya ke bayyana cewa saboda ya goyawa shugaba Buhari baya a 2015 ne ya sa ya lashe zabe.

"Obasanjo ya ce shugaba Buhari ba zai ci zabe ba a karo na biyu, kuma sai gashi shugaba Buharin ya ci zaben. Shin, ba na taba cewa Obasanjo sai ya ji kunya a kasar nan ba idan aka bayyana sakamakon zabe. Nasarar shugaba Buhari ta nuna cewa Allah ne mai ba da mulki."

Sarkin ya yi kira ga 'yan Najeriya da su goyawa shugaba Buhari baya, ya ce matsalolin rashin tsaro, rashin aikin yi da sauran kalubale da ake fuskanta a kasar nan, za a kawo karshen su ne idan al'umma ta hada karfi da karfe da gwamnati.

KU KARANTA: Wani mutumi ya roki manyan Arewa su hana al'adar Hausawa ta aurar da yara kanana

Ya kuma shawarci Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, da ya janye karar da ya shigar kotu akan zaben shugaban kasa.

"Idan akwai wani wanda yake da kusanci da Atiku a nan gurin, to ya sanar dashi cewa ba zai taba samun nasara a kotu ba," in ji shi.

"Buhari zai kammala mulkin sa a ofis, amma kuma shima Buhari dole ne ya saurari abubuwan da mutane ke fada, ya dinga addu'a kuma ya kasance mai gaskiya a dukkanin al'amuran shi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel